Tarihin Fatima Zahra [a.s]



An ruwaito daga Asma'u tanacewa: 'LokacindaFatimazata yi wafati. ta ce ma Asma'u: "Lallai Jibrilu ya zo ma Manzo da kafiir na Aljanna lokacin da zai yi wafati. Sai Manzo ya kasa shi kashi uku. Daya nasa. daya Aliyiu sannan ni kuma daya...Ya Asma'u ki je gun kaza za ki gan shi ki dauko min' Bayan Asma'u ta kawo mata. sai ta mike ta yi wanka ta yi alwala. Sannan ta ce Asma'u ta dauko mata turare da tufafin da take salla da shi. Bayan ta shafa turaren ta sanya tufafm. sai ta ce 'Asmau idan na yi sujuda ban dago ba ki kira sunana. ldan ban amsa miki ba. to ki sani na koma ya zuwa gurin Ubangijina. na hadu da Mahaifina! Lokacin da Asmau ta kira ta sai ba ta atnsa mata ba. ko da Asma'u ta zo ta duba sai ta ga hakika Fatima (AS) ta bar duniya! Sai ta aigumc ta tana sumbaiitaiia tana kuka Ana cikin haka sai Hasan da Husaini suka shigo. Sai suka ce wa Asma u "Umminmu barcin me takeyi a wannan !okacin'r Sai Asma'u ta ce: 'Ya 'ya'yan Manzon Allah. Umminku ba barci take yi ba. hakika ta bar duniya ne. Sai Hasan ya fadi ajikinta yana sumbantar ta yana kuka. yana cewa: "Ya Ummi ki yi min magana tun kafin rahina ya rabu da jikma! Shi kuwa Husaini yana sumbantar ta yana cewa:  Nine danki Husaini. ki yi min magana kafin zuciyata ta fashe!"

Sai Asma'u ta ce: "Ya yayan Manzon Allah ku je ku fada ma Mahaifinku cewa Mahaifiyarku ta rasu " Bayan sun kusa da masallaci sai suka daga sautinsu. suna kuka suna cewa "Umminmu ta yi wafati ta bar duniya! Ko da Aliyu (as) ya ji. sai ya fadi yana mai sujuda yana cewa: "Gun wa zan yi ta'aziwar yar Manzon Allah? Da na kasance ita nake wa ta aziwar Manzon Allah. yanzu kuma gun wa zan yi ta’aziyya?'

(AS)CIKIN KABARINTA!!

Ba ka jin komai sai kuka cikin gidan Aliyu (as). Mutanen Madina ko'ina da ina sai kuka. Matan Banu Hashim dukkansu sun hadu cikin gidan suna ta kuka. Imam Aliyu (as) yana zaune. a tare da shi akwai Hasan, Husaini, suna ta kukan rabuwa da mahifiyarsu. Ita kutna Ummi Khulsum ta fita waje tana kuka tana cewa: "Ya Babanmu, Ya Manzon Allah, hakika yau kam mun rashe ka dukkannin rasawa, babu saduwa nan duniya har abadaF Su kuwa mutane sai zuwa suke ba iyaka suna yi wa Imam Aliyu (as) ta?aziwa. Sai Abubakar da Umar suka ce: In za a yi mata salla a bari sai sun zo ko kuma a aike musu. Nana (as) ta yi wafati ne bayan la’asar zuwa magriba. Lokacin da jama'a suka ga dare ya yi ba a yi mata salla ba, sai suka yi zaton jana'izar sai gobe za a yi, don haka sai suka watse. sai wadanda aka sanar da su yadda abin yake kawai suka tsaya. Cikin wannan daren Imam (as) ya yi mata wanka, Asma'u tana zuba mishi ruwa, sannan ya sanya mata likkafaninta. Lokacin da dare ya yi nisa sosai mutane sun yi barci. sai Imam ya kira jama'arsa suka yi wa Nana (as) salla. wanda suka hada da: Salmanul Farisi. Ammar Ibn Yassir. Abu Zarri Gifari. Mikdad. Huzaifatul Yamani. Abdullahi Ibn Mas'ud. Abbas Ibn Abdulmuttallib. Fadeel Ibn Abbas. Akilu. Zabair Ibn Ayywam, Buraida da wadansu 'yan jama'a daga Banu Hashim1 Imam Aliyu (as) ya shige gabadonyayi wa diyar Manzon Allahsallah. yanatnai cewa: "Ya Ubangiji 'yar Manzonka ta yarda da ni. ya Ubangiji. hakika ta fayu cikin kawaici. ka yaye mata. Ya Ubangiji an kaurace mata ka sadar da lta Ya Ubangiji hakika an zalunce ta ka bi mata hakkinta. kai ne mafi alkhairin masu hukunci." Sannan sai ya yi mata salla raka'a biyu. ya daga hannuwansa sama yana cewa: "Wannan yar Manzonka ce Fatima. ka fitar da lta daga duhu ya zuwa haske .."

An samu ruwayoyi daban-daban danganc da mda kabann Nana (as) yakc. Wasu sun tafi a kan yana Baki'a. Wasu kuma sun tafi a kan yana cikin dakinta. lokacin aka fadada Masallacin Manzo sai ya zama yana cikin Masallacin Manzo. Ala ayyi halin dai kabarm ya buya kamar yadda ta bar wasiyya. Wanda wannan kadai ya ishi mai karatu tunani a kai. me ya sa haka ta faru9 In ba dalili. me ya sa yanzu bai iya zuwa  Madina ya ce ga barin 'yar Manzon Allah?

Bayan an haka mata kabari, sai Imam (as) ya shiga cikin kabarin sannan Abbas da dansa Fadeel suka mika mishi ita ya sanya ta cikin kabarin. hawaye suna ta zubo masa bi da bi! Bayan ya sanya td sai ya ce: "Ya kasa ga amana nan na ba ki. Wannan ita ce diyar Manzon Allah. Da sunnan Allah Mai Rahma. Mai jinkai. Da sunan Allah bisa Millan Manzon Allah. Ya SIDDIKA! Na mika ki ya zuwa wanda kika fi kauna da ni, na yardar miki da abin da Allah ya yardar miki da shi."

Sannan ya karanta inda Allah yake cewa: "Daga gare ta muka halitta ku, cikinta za mu komo da ku, sannan mu fito da ku wani lokacin" Sannan sai ya fito daga cikin kabarin. sai suka mayar da kasa kanta! Sun rufe ragamar Annabta! Sun nifc shakshya ta farko cikin iyalan Manzo! Sun rufe macen Aljanna a surar 'yan Adam! Sun mfc

Bayan nan sai Imam Aliyu ya tsaya a kan kabarinta yana kuka yana cewa cikin wake:

(1) Kowa ne haduwa ta masoya akwai rabuwa bayanta Duk abin da bai kai ga mutuwa ba kadan ne Rabuwata da Fatima bayan Mahaifinta. Dalili ne a kan masoya ba sa dawwama.

(2) Rabuwa da ke shi ne mafi girman al amura.Rabuwa da ke Fatima shi ne mafi girman bakin ciki. Zan koka. kokawar asara da bakin cikin rabuwa da masoyin da ya fi kowa nko da sunna madaidaiciya Ku taimaka min ya idanuwana don bakin cikina da kuka madawwami a kan masoyiyata.

(3)  Masoyiya ce wacce ba a gama ta da wata masoyiya Babu sauran wata abar kauna a zuciyata banda ita Masoyiya ce ta buya daga idanuwana da jikina Amma ba a bar buya b ace a cikin zuciyata.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 next