Tarihin Fatima Zahra [a.s]



Lokacin da Manzo ya ga za ta cika. sai ya ce mata 'Ya Khadija in kin je ki isar da gaisuwata zuwa ga yan uwanki." Sai ta kallc shi kallo na kauna da bankwana ta ce "'Su wauene "yan uwana ya Rasulullah, Sai ya ce "Maryam binti Imran da Khulsum yar uwar Musa (as) da Asiya matar Fir'auna." Sai ta yi murmushi ta ce "Zan lsar ya Rasulullah. '

Sai Manzo ya ce mata an umurce ni da in yi miki albishir da gida a Aljanna na lu'u-lu'u. babu hayaniya. babu tashin hankali ko kadan a cikinsa. Nana Khadija (as) ta yi shahada tana da shekara sittin da uku a duniya An binne ta a'wani guri wanda a ke-kira "HAJJUN'". Bayan an haka kabarin sai da Manzo (as) ya shiga ciki yana kuka. ita kuma Fatima (as) tana kuka tana kekkewaya shi.

Bayan an dawo daga rufe ta Nana (as) takan dinga rike hannun Mahaifinta tana tambayarsa ina Umminta? Sai ya kalle ta ya yi murmushi. Wata rana ta ce "Ina Ummina'7" Sai Mala'ika Jibnli ya zo ya ce wa Manzo 'Ubangijinka ya umurce ka da ka isar da gaisuwarsa zuwa ga Fatima da murjan tare da Asiya matar Fir'auna da Maryam binti Imran." Ko da Manzo ya gaya mata wannan sakon, sai ta ce "Allah (swt) shi ne aminci. Daga gare shi aminci yake zuwa kuma gare shi aminci yake komawa." Allahu Akbar!

Kafin mu ci gaba idan mai karatu ya lura mun yi kokarin bin abin daki-daki wajen fito da kadan daga cikin abubuwan da suka faru tun daga asalinta zuwa daukar cikinta zuwa haihuwa, sai kuma zuwa shekarunta wanda ta yi a nan duniya, 18, masu cike da dimbin tarihi da ababen aja'ib. wadanda alkalumma sun yi kadan su zo da shi, sai dai kamantawa. A shekarunta na farko zuwa na biyu, ta yi sune a gidan Mahaifinta, inda aka haife ta kafin shiga kurkuku. Sannan ta yi shekaru uku a kurkuku. Bayan sun koma gida kuma ta yi shekaru uku sannan sai hijira zuwa Madina tana da shekaru takwas a duniya. Yanzu za mu zo da kadan daga abin da ya saukaka cikin shekaru uku bayan fitowarsu daga kurkuku. Insha Allahu (swt).

 

BAYAN FITOWA DAGA KURKUKU

Bayan wafatin Nana Khadija (as) da Abu Talib (as) rayuwar Manzo ta canzakwarai dagaske ta wajen fuskantar matsaloli daban-daban dabakin ciki iri-iri. Wanda a gida ya rasa Khadija (as) a waje kuma ya rasa Abu Talib (as). ya rasa kuma wanda zai tsaya a makwafinsu wajen ba shi kariya. shawara da lallashi. Sai karamar diyarsa Fatima (as) wadda ba ta fi shekara biyar a duniya ba. Kuraishawa sun matsa ma Manzo a wannan lokacin sosai. Duk abin da suka kasa yi a baya saboda tsoron Abu Talib (as) a yanzu sun samu dama na yin hakan. Har sai da ta kai ga suna watsa mishi kasa a kai. ko kashin tumbin akuya yana salla.

Wata rana Manzo yana salla ya yi sujuda a Ka'aba sai wani daga cikin mushrikai yaje ya zuba masa kasa a kai. Lokacin da Manzo ya shigo gida sai Fatima (as) ta ga kasa a kansa, sai ta debo ruwa tana wanke mishi tana kuka. Shi kuma Manzo yana gaya mata yana cewa "Kar ki damu Allah (swt) mai taimakon Mahaifinki ne."

An ruwaito daga Ibn Abbas yana cewa: Wata rana Manzo mai tsira ya shiga kaaba yana salla. shi Abu Jahal ya ce wanene zai je in Manzo ya yi sujada ya jefa mishi kashin tumbin akuya, ya bata mishi sallarsa?" Sai wani mai suna Ibn Zabari ya ce shi ne. Sai ya amsa ya je ya jefa wa Manzo a kai yana sujuda!!!  Aka rasa wanda zai je ya dauke sai ya yi musu addu'a dukkansu suka halaka a yakin tiadar. Bayan wannan Fatima (as) ta zo ita da mahaifinta gida tana wanke mishi tana kuka. Saboda ire-iren wadannan hidimomin ne da Fatima (as) take yi wa Mahaifinta wanda ba wani sai ita yake kiran ta da suna UMMI ABIHA (Urnmin Mahaifinta).

Sani Katsina cikin baitin waka yana cewa: Nana 'yar Ma'aiki Azzahara, Ba kamarki Nana Fatimatu. Yakan kira ta Ummi Abiha. In har zai yi zance Fadimatu. Ya Nana kama hannuna, Ki kai ni gun Ma'aiki Fadimatu. Domin in warke cututtukan da ke bin nafsiyatu. Nana "yar Ma'aiki Azzahara Ba kamarki Nana Fadimatu.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 next