Tarihin Fatima Zahra [a.s]



Ya Ummul Hasanainu ya Khaira Nisa'il alamina Batula.-Amshin wakar kenan.

2.  Tun kafin ayo duniya Zahra da ma akwai ta,

Hasken Manzonmu ce. shi ko hasken Allah ku fahimta, Ka san ko Muhammadu tun kan a yi Adamu ya gabata, Zahra maujudiya ce a haske tun kafin halitta.

3.  Ko nan na tsaya ka san Zahra'u ba kamarta,

Duk duniyarmu da lahira Fatima ita ce karshen sarauta. San da Rasulu ya yi mi'iraji ya ce mana ya gano ta. Zahra'u ko cikin Firdausi daban ne matsayinta.

4. A cikin Aljanna ne na ga wata mace mai jin sarauta.
Ta sa kambun sarauta Hurul in ne hadimanta.
Misalinta da hurulin taurari ne da wata.

Da na ce wacece sai aka ce Zahra ce 'yarka Binta

5.  Kowaz zo duniya in an circ Annabi walidinki.
To ke ya rako da Ali da Hasan da Husaini danki.
Duk duniyar ga kogi ce ba jirgi sai fa naki.

Duk wanda ya ki ya hau. to ya hallaka in ya bar ki

6.  Ayoyin da Allah ya saukar sun fi dubu a kanki.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 next