Tarihin Fatima Zahra [a.s]



RUKAYYA BINT MUHAMMAD (as)

Bayan haihuwar Nana Zainab (as) da shekara uku. sai Allah (swt) ya kara azuita Maiizo da haihuwarNana Rukayya (as) ma'abuciyar kyau. W'adda duk 'yayan Manzo ba mai kyawunta. barc cikin garin Makka sai Nana Fatima (as) don lta kirar matan Aijanna ce. Nana Rukayya (as) us taso cikin gidan Manzo har zuwa girmanta. wanda dabi » masu kyau ba sai iia kai ga ma fadi ba. don sananncn abu ne da ba zai boyu ga kowa ba

Manzo ya aurar da Nana Rukayya (as) tana da shekara sha daya. gawata ruwayarkoshabiyu, Gawata mwayar. ga l'taibata Ibn Abiiahabi Lokacin auren Nana Rukayya (as) ba a yi shagali kamar na Nana Zainab (as) ba don mahaifharta ba ta son aurcn sosai. saboda ganin za a kai "yartagidan Abiiahabi. kumaba sishiri da matar Abilahabi uwar Utaibat. 3 saboda munanan halayenta, wanda'ba ya boyuwa ga kowa. Ya zo a cikin tarihi cewa tunda Manzo ya auri Nana Khadija (as) ita matar Abilahabi take bin bokayen garin Makka da kewaye a kan tana so auren ya rabu. Daga karshe wata wacce ta shahara gun bokanci ta gaya mata cewa wannan auren ba zai rabu ba har abada. Kuma zuriyar Manzo za su fito ne daga tsatsonta. Ko da ta ji haka, sai bikin ciki ya kama ta, ta sa aka dinga yi wa warihan bokar azaba, wanda ya zama sanadiyyar mutuwarta.

Bayan an yi auren, sai Allah (swt) ya saukar wa Manzo wahayi. kuma ya umurce shi da ya bayyanar da sakon Allah (swt) ga jama'ar Kuraishu. Bayan Manzo ya tara su ya yi musu gargadin azaba mai radadi in ba su yi imani ba, sannan kuma su shaida cewa shi Manzon Allah ne, sai Abilahabi ya yi la'anta ga Manzo yana cewa "a kan wannan ne ka tara mu?" Bayan Abilahabi ya ki yin imani, sai ya ci gaba da cutar da Manzo. har Allah (swt) ya saukar da: "Hannaye biyu na Abilahabi sun halaka, shi ma ya halaka. Dukiyar da ya tara ba ta amfana masa komai ba,"

A wannan ranar Abilahabi ya kira Utaibatu da dan uwansa Utuba. wanda shi yake auren Nana Ummu Khulsum (as) ya ce musu "Ba ni ba ku har abada matukar kuna tare da 'ya'yan Muhammad ba ku sake su ba.' Nan take suka sake su. Bayan sakin kuma. sai Utaibatu ya biyo Manzo har gida da bulala a hannunsa. Ya sami Manzo ya gaya masa bakaken maganganu. ya kuma yaga masa nga bayan ya shauda mishi bulalar. sannan ya juya ya tafi.

Sai Manzo ya yi mishi addu'a ya ce "Ya Allah ka hada shi da karc daga cikin karnukanka." Nan takc Allah (swt) ya amsa ma Manzonsa Wata rana Utaibatu ya tafi fatauci Sham da wasu jamaar Kuraishu. sai zaki ya taso masa ya yi kuwwa, jama'a suka cece shi. aka kon zakin Bayan dare ya yi kowa ya kwanta. sai wannan zakin ya dawo yatsallaka duk jama'an da ke kewaye da shi har ya isa gare shi ya damke shi ya halaka shi. Rundunonin Allah ba su da iyaka, kowa ya ja da addini sai buzunsa!

Bayan rabuwar Nana Rukayya (as) da Utaibatu. sai ya aurar da ita ga Usman Ibn Affan. Ta yi hijira da mijinta zuwa Habasha. lokacin da Manzo ya yi ma musulmi umurni da su yi hijira zuwa Habasha saboda tsanantawar da kafirai ke yi ma musulmi. Lokacin da Nana Rukayya take Habasha. samann Habasha suna ta damun ta da kallo. saboda kyawun  halitta da Allah (swt) ya yi mata, har ma ta yi musu addu’a suka naiaKa.

Nana Rukayya (as) ta haifar ma Usman Ibn Aflan da da a Habasha akasa mishi suna Abdullahi.Bayan hijira zuwa Madina Allah (swt) ya yi ma Abdullahi rasuwa yana dan shekara shida, yayin da wani zakara ya fasa mishi ido har fuskarsa ta kumbura har ya zama sanadiyyar rasuwarsa. Wannan ya haifar ma Nana Rukayya da bakin ciki mai yawa wanda ya sa ta kamu da ciwo har ya kai ta ga rasuwa. Usman Ibn Affan shi ne ya yi jinyarta bisa umurnin Manzo, don haka bai samu zuwa yakin Badar ba. Bayan ta rasu, ya yi mata wanka ya kuma binne ta, tana da shekara ashirin da daya a duniya.

 

UMMU KHULSUM BINTI MUHAMMAD (SAW)



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 next