Tarihin Fatima Zahra [a.s]



1. An ba ka suriki kamar ni, ni ba a ba ni ba.

2. An ba ka mata Siddika. 'yata, wanda ni ba a ba ni mace irinta ba. iii.  An ba ka Hasan da Husaini "yayanka wadanda ni ba a ba ni "yaya lrinsu ba. Sai dai ku duka (Aliyu. Fatima Hasan, da Husaini) daga gare ni kuke. ni kuma daga gare ku nike. Sai na ce watau su duka abu guda ne wanda ba a iya rabewa.

Wata rana Mufdal dan Amru ya tambayi Imam Ja'afar cewa yyanene ya yi ma Fatima (as) wanka bayan wafatinta? Sai Imam Ja'afar (as) ya ce masa Imam Aliyu ne. Sai ya ga alamar kunci tare da shi. Sai ya ce masa kana jin kunci ne9 Sai ya ce na'am, Mahaifina fansanka ne. ya Shugabana. Sai Imam Ja'afar (as) ya ce masa ita Fatima Siddika ce babu wanda zai mata wanka sai Siddiki. ba ka ga Annabi Isa (as) shi ne ya yi ma Maryam (as) wanka ba?

 

"c MUBARAKA (as)

Albarka, tana daukar ma'anoni da dama. Wasu daga cikinsu sune: karuwa. yalwa. rabauta. da sauransu. Akan ce ma abu ne yana da albarka in ya zama mai karuwa da amfani.

To dangane da aramarin Nana Fatima (as) wannan ba boyayyen abu bane ga kowa da kowa. Hakika Allah (swt) ya sanya naui-nauin albarka mai yawa ga Nana Fatima (as). Daga ciki shi ne ta yadda ya sanya zumar Manzo baki daya ta hannunta. A nan muna iya ganin cewa lta kadai ce jrntn Manzo a bayan kasa bayan wafatinsa. har ana mata lakabi da bakiyatun nubuwwa" (Ragowar Annabci) ita kumata yi wafati ta bar 'ya'ya hudu da Imam Hasan. Itnam Husain. Sayyida Zainab da Sayyida Rukayya. Sannan Wakfar Karbala ta zo. aka kashe "ya'yan Imam Hassan (as) guda bakwai. Aka kashe Imam Husain (as) da yayaasa baki daya. Sai Zainul Abidin ne kadai ya yi saura. shi ma don ba shi da lafiya ne Aka kashc 'yayan Zamab (as) su biyu. ita kuma Ummu Khulsum da ma ba ta taba haihuwa ba. don wani hikima na Allah (swt). An yi nufin share zunyar Manzo ne a bayan kasa. amma Allah bai yarda ba. 'ya'yan mikiya sun gagari shaho.

Daganan kuma sai aka kama kisan gilla da dauri har ma da rataye ga duk wani daga cikin zuri'ar Manzo. kai ka ce Manzo da zai yi wafati ya bar wasiyya ne a kan haka. wanda ya zama tilas don kar a saba mishi. kamar:

 

WAKI’AR HARRA:



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 next