Tarihin Fatima Zahra [a.s]



Mahaifinta ya yi wafati a Madina yana da shekaru sittin da uku a duniya. Shi ne wanda Umar Ibn Khaddab ya nmaito Mala'ika Jibnlu ya hada gyyiwow insa da nasa ya daura hannunsa a kan cinyarsa ya ce ya ba sln labann Musulunci. Shi ne wanda Annabawa da Manzanni suka yi sahu a masallacin Kudus ya zo ya yi musu salla Shi kadai ne duk cikin halitta wanda ya taba kai wa magaryar tukewa a can sama ta bakwai. sannan ya gana da Ubangijinsa

Ya rasulullah mun koka da abin da Fatima (as) ta koka da shi na wafatinka Muna fushi da abin da ta yi fushi da shi. mun yarda da abin da ta yarda da shi. Kuma muna taya ka bakin cikin abin da ya same ta da zuriyarta bayan ba ka Ya Raiulullah mun mika ta'aziwar wafatinka ga 'yarka (Fatima) (as). Muna mika ta'aznyar Imam Husaini (as) ga Imam Khomcini (r.a) Sannan muna mika ta'aziwar Wafatin Fatima ga Malam Ibrahim Yakub Zakzaky (h). Ya Allah ka sanya mu cikin ceton Nana Fatima da Mahaifinta in kiyama ta tsaya. amin summa amin.

 KASO NA UKU

FATIMA (AS) BAYAN WAFATIN MAHAIFINTA

Tun tasowarta har zuwa girmanta har aurenta ba ta taba rabuwa da Mahaifinta ba. wanda ya kai tsawon kwana goma. Manzo bai iya yin barci har sai ya gan ta ya sumbance ta. Har wata rana A'isha ta ce "Ya Rasulullah kana sumbantar ta alhali tana da miji?" Sai ya ce "Wannan tsoka ce daga gare ni, ruhina ne wanda ke cikin jikina. Koyaushe na ji begen Aljanna sai na sumbace ta domin ita macen Aljanna ce a sura ta dan Adam." Ta shaku da Manzo matukar shakuwa, ya zama shi ne tunaninta, madubin kallon ta kodayaushe. Yau ga shi ba ta ganin shL babu kuma inda za ta kuma ganin shi a sararin duniyar nan baki daya. Bakin ciki da damuwa ba sai an fada ba.

An ruwaito daga Fizza (mai yi wa Fatima hidima) tana ba da labarin bakin cikin Nana bayan wafatin Mahaifinta. tana cewa: "Lokacin da Manzo ya yi wafati babu wani wanda za ka hadu da shi. yaro ne ko babba face cikin kuka dumu-dumu. Babu wani masoyin Manzo. makusanci. waliyyi a bayan kasa wanda bakin cikinsa ya kusa da na Sawada Fatima (as).

"Kwananta bakwai cur a gida ba abin da take yi sai kuka da tuna rayuwar Mahaifinta. A kwana na takwas ne ta kasa juriya har sai da ta fito waje ta koka kokawa mai tsanani. sai da duk mutanen Madina suka fashe da kuka. Tana tafiya tana kuka tana cewa:

Ya Babana. ya Zababbena. ya Muhammadu! Ya gatan marayu da tsofaffi! Wa ka bar wa Alkibla da masallaci? Wa ka bar wa diyarka?" Har ta iso inda kabarin Mahaifinta yake. Ko da ta kalli kabarin. sai ta fadi ta suma. Matan da ke gurin suka yi maza suka yafa mata ruwa har ta farfado.

Tana farfadowa sai ta kama cewa: Karfma ya kare. fatar jikina ya motse. makiya sun yi min dariya. furucina ya kare. Ya Babana na zama ragowa cikin kawaici. zantukana sun kare. gadon bayana ya karye. rayuwata ta gurbace. zamani ya yi tsawo a kaina. Ya Babana ban sami wani mai debe min kewa ba bayanka. Ban samu mai share min hawaye ba. ba mai taimaka min a kan raunina. Hukunci ya dauke bayanka. Mun daina jin saukowar Jibrilu da Mika'ilu. Komai ya yanke bayanka. shaukina da bakin cikina gareka ba mai yankewa ban e..

Bayan nan sai ta ci gaba da cewa:Ya Babana! Hasaken duniya sun bice tare da wucewarka, fiiranni sun yi yaushi bayanka.

Ya Babana! ba zan gushe ba cikin bakin ciki har sai na riske ka. Ya Babana! Wa ka bar wa miskinai da marayu. Ya Babana! Me ka bar wa al'ummarka har zuwa tashin kiyama. Ya Babana! Mun wayi gari bayanka cikin masu rauni. Ya Babana! Mun wayi gari mutane sun watse mana. bayan sun kasance kewaye da mu zamaninka.

Wane hawaye ne ba za su zubo ba bayan rabuwa da kai? Wane bakin ciki ne ba a gani ba bayan rabuwa da kai? Wane kwayan ido ne zai rintsa bayan rabuwa da kai,Kai ne mai rayar da addini. kai ne hasken annabta. Me ya sa duwatsu ba su gushe ba? Me ya sa kogilna ba su kafe ba?



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 next