Tarihin Fatima Zahra [a.s]



Bayan kisan gillar Ha Yazid Ibn Mifawiyya ya yi a Karbala sai da kuma ya sakc aikcwa da rundunonin yaki na mutum dubu talatin zuwa Madina mishi cewa iyalan Manzo bayan Karbala sun koma Madma da zama. Ya je Madina ya halatta mishi duk abin da ke cikinta na dukiya, mata, yara da sauransu, kuma duk abin da zai yi ya yi kokan ya gama shi a cikin kwana uku.

Muslim Ibn Ukba ya nufi wajen Madina, su kuma mutanen Madina labari ya riske su, don haka suka shirya suka fito wajen Madina zuwa wani guri wanda ake kira 'HARRA. Ko da rundunar Yazid suka iso gurin, sai yaki ya kaure. Amma ina! Sarkm yawa ya fi Sarkin karfi domin ba su yyuce 'yan daruniwa ba.

Bayan da rundunonin Yazid suka yi musu kisan gilla sai suka shigo cikin garin Madina suna ta kisan yara da manya da tsofaffi da kumj diban dukiyoyi, don babu gidaft da ba su shjga ba sun kashe duk abin da ke gidan mai rai. har kaji da tantabaru!

Sun shiga gidan Abi Sa'idul Kuduri. Sahabm Manzo. a lokacin ya tsufa ba ya gani. suka kama shi suna tsige mashi gemu. suna azabtar da shi. yana lhu yana cewa shi ne Abi Sa'idul Khuduri. Sahabin Manzo. amma ina ba su san shi ba don ba su taba jin sunaii ba. Suka kama dabbobin gidansa suka yanka baki daya sukajefa cikin njiyar gidan!! Sannan kuma suka shiga wani gida suka tarar da wata mace tana shayar da danta. suka sa wuka suka yanka shi. nonon mahaifiyarsa yaria bakmsa!! -Bayan su kashe Mahaifmsa a cikin gidan.

Bayan wannan kuma duk wata budurwa wacce suka gan ta sai sun yi mata fyade! Sun yi wa 'yan mata sama da dubu fyade a wannan lokacin. An ruwaito cewa a wannan shekaran an haifi yara sama da dubu a Madina wadanda ba su da ubanni!! Sannan sai Kwamandansu ya yi musu izini da su je masallacin Manzo, duk wanda ya guda zuwa wurin bai tsira ba, su kashe shi ko wanene. A wannan lokacin sai da jinin mutane ya yi lebil da kabarin Manzon Allah (swa)H! WAKI'AR ZAID IBN ALIYU IBN HUSSAIN (as) Bayan wafatin Mahaifinsa (Zamul Abideen) gudun kar a yi mashi bafa Banu Umayya suka shirya rundunonin yaki dubu arba 'in, don su yake shi. Shi kuma yana da mabiya wadanda suka yi mishi bai'a dari uku A haka suka kwama da wannan runduna ta 40.000 din kwana da kwanaki har Allah (swt) ya yi musu nasara da samun shahada baki daya. babu wanda ya yi saura har shi Zaid din (as). WAKI'AR FAK;

Bayan waki'ar da muka bayyana sai kuma wacce ta bi mata watau waki'ar Fak. Shi Fak wani yyuri ne inda waki'ar ta faru, wanda sai da aka mayar da wurin tamkar mahauta saboda kwararan jinin 'ya'yan Manzo da mabiyansu. Kai in takaice ma sai da ta kai duk wani wanda aka ji ya ambaci Imam Aliya (as) da wani alkhairi sai a kama shi a ce dan Shi'a ne. ko a zo masallacin Manzo a Madina a tsire shi ko kuma a kore shi daga garin. a kwace gidansa da dukiyoyinsa ko tna a rusa gidan. Kai akwai wadanda aka sa ma gidajensu yyuta suna ciki suka kone. akwai wanda ya yabi Imam Aliyu (as) a baiti na wake aka yanke harshensa aka kuma binne shi da rai

Wata rana su Banu Umayya sun kira Imam Nisai (ra) cewa ko akwai wani hadisi da yake bayyana falalar babansu (Mu awiyya)? Sai ya ce a'a, sai dai inda wata rana Manzo ya aika mashi da ya zo ya yi rubutun wahayi. da aka saukar. sai ya aiko wa Manzo a kan ba zai zo ba yana cm abincu sai Manzo ya ce kada Allah ya sa ya koshi. Daga nan sai ya zama bai koshi. a karshe yunwa ce ta kashe shi. Ko da ya fadi haka. sai suka fusata suka sa aka dinga tattaka shi bar sai da hakarkannsa suka sassaba. daga karshe ya samu sahada!

To abin da muke cewa a nan shi ne duk da irin wadannan ayyukan ta'addanci na Allah wadai da kisan gilla da sarakunan Musulunci suka dinga yi daya bayan daya ga halan Manzo da Shi'arsu. wannan bai hana Allah wanzar da ya yan Fatima (as) a bayan kasa ba. Saboda aibarkar da ya yi mata da kuma cikar zancensa, inda yake ce ma Manzo "Lallai mun ba ka Alkausar" Watau abu mai albarka. Shi ne haihuwar Nana Fatima (as).

A yanzu haka akwai "ya'yan Fatima (as) a sassa daban-daban na duniya sama da miliyan taiatin da biyar (35.000.000). Wanda a yanzu ana iya gane su da atamoninsu. kamar a Iran ana iya ganin su da bakaken rawunna.

 



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 next