Tarihin Fatima Zahra [a.s]



HUDUBAR NANA FATIMA (AS) A MASALLACIN MANZO (SAAW)

"Dukkan yabo ya tabbata ga Allah bisa ga abin da ya ni'imta da godiya bisa ga abin da ya sanar. da yabo bisa ga abin da ya gabatar na daga gamewar nrimomin da ya kirkira da manyan ni'imomin da ya ban da cikar kyaututtukan da ya jibintar. wadanda yawansu ya fi karfin kidddigewa, daduwarsu ta nisanta daga sakamako, dawwamarsu ta nisanta daga idraki. Ya kira su domin neman karin godiya ga dorewarsu, ya nemi godiya daga talikai ta hanyar yawaita su. ya kuma biyantar da kiran zuwa makamantansu.

"Ina shaidawa babu abin bautayya da gaskiya sai Allah. Shi kadai yake ba shi da abokin tarawa. kalma ce da ya sanya ikhlasi shi ne mai tawilinta. ya cusa ma zukata isa ga ma'anarta. ya haskaka fahimtar ta a cikin tafakkuri. wanda ganin sa ya hanu daga idanuwa. siftanta shi ya hanu daga hankula. ya samar da abubuwa ba daga wani abu da ya kasance kafinsu ba. Ya yi su ba tare da kwaikwayon misalin da ya misalta su a kansa ba Ya kaskantar da su ne da lkonsa. ya halitta su a bisa ganin damarsa ba tare da yyata bukata ba daga gare shi a kan kasantar da su ko wata fa'ida a cikin kamanta su. sai dai kawai domin tabbatarwa ga hikimarsa da fadakarwa a kan biyawa gare shi da bawanar da ikonsa da bautarwa ga bayinsa da daukakaw a ga da ayyarsa Sannan ya sanya lada a kan biyawa gare shi. ya s-anya azabtanya a kan saba masa domin kiyaye bayinsa daga ukubarsa da kuma kaunar saduwarsu da Ajannarsa.

"Kuma ina shaidawa Babana Muhammad bawansa ne kuma Manzonsa ne. ya zabe shi. ya kuma kiyaye shi kafin ya aiko shi. ya ambace shi kafin ya zabe shi Ya tsarkake shi kafin ya tayar da shi a lokacin da talikai suna kasantattu da gaibi. katangaggu da suturun razani. kuma suka kasance gwame da matukar rashi saboda ilimin Atlah a kan karshen al'amurra da kewaycwa da faruwar zamunna da masaniya ga wuraren aukuwar kaddara.

"'Allah Ta"ala ya aiko shi ne domin cikawa ga al'amarinsa da himmatuwa a kan gudanar da hukuncinsa da kuma zartarwa ga kaddarorin cikarsa. Sai ya ga aliimmu sun rarraba a cikin addinansu. kifaffu a kan w utaccsu. masu bauta ga gumakansu. Sai Allah Ta'ala ya haskaka duffansu da Babana Muhammad (SAW). ya yaye ma zukata matsalolinsu, ya gusar ma idanuwa da makantarsu: ya tsayii da shiryarwa a cikin mutane. ya tsamar da su daga bata, ya warkar da su daga makanta, ya shirya da su zuwa ga daidaitaccen addini. ya kira su zuwa ga mikakken tafarki. Sannan Allah ya karbe shi karbar tausaya^ya da zabi da kauna da fifitawa. Lallai a yanzu Muhammad yana cikin hutawa daga gajiyar wannan gida. An kewaye shi da managartan Malaiku da yardar Ubangiji mai yawan gafara, da makw abtakar Sarki mai rinjaye. Allah ya yi tsira ga Babana. Annabinsa. zababbensa daga talikai kuma yardajjensa. Aminci da rahmar Allah da albarkarsa sun tabbata gare shi."' Daga nan sai ta juya kan wadanda suke zaune ta ce:

"Ya bayin Allah! kune ahalin umurninsa da haninsa. kune makiyayan addininsa da wahayinsa. kune aminan Allah a kan ka-yyunanku. kune masu isar masa ga sauran arummu. Shugaban gaskiya gare shi a cikinku yakc. alkawari ne ya gabatar da shi gare ku. kuma wanji ne da ya halifantar a kanku Littafin Allah mai magana. Alkurani mai gaskiya. haskc mai daukaka. fitila mai haskakawa. hujjojinsa a bawane suke. asiransa a fili suke. zahiransa a sarari sukc. matsayin mabiyansa abin buri ne. biyawa gare shi |agora ne zuwa ga samun yardar Allah. Sauraron sa mai kanya ne ga samun tsira. da shi ne ake samun hujjojin Allah masu haskc. ake ganc fassararrun fanllansa da haramtattun abubuwan da ya tsawatar. da bawanannun falalolinsa da gamsassun dalilansa da iiuistahabban falalulinsa da saukakan abubuwan da ya yi baiwarsu da kuma wajibabbun shari'o insa

"Sa: Allah ya sanya (wajabta) lmam domin tsarkakewa gare ku daga shirka. da salla domin tsaftaccwa gare ku dagagirman kai. da zakkah domin tsarkakewa ga rai da karuwar arziki. da azumi domin tabbatarwa ga ikhlasi. da hajji domin karfafawa ga addini. da adalci domin natsarwa ga zukata. da biyawa gare mu domin tsari ga arumma. da imamancimu (shugabancinmu) domin amintuwa daga rarraba. da jihadi da izza ga Musulunci da kaskantarwa ga ahalin kafirci da munafunci. da hakuri domin taimakawa a kan cancantar lada. da horo da kyakkyawa da hani ga mummuna domin maslahar kowa da kowa. da kyautatawa ga mahaifa domin garkuwa daga azaba. da sadar da zumunci domin yalwatawa ga rayuwa. da kisasi donnn kiyay ewaga zubar da jini. Da cika bakance (nazar)domin bijirowa ga satnun gafara. da cika maaunai da ababen gwaji aomin musam awa daga tauyewa. da hani ga shan giya domin tsarkakewa daga dauda, da nisantar kazafi domin hijabantuwa daga la'anta, da barin sata domin cancantar ingantattar lafiya. kuma Allah ya haramta shirka domin tsarkakewa ga rububnya,'Saboda haka ku ji tsoron Allah hakikanip tsoron sa. Lallai kada ku mutu sai kuna musulmi' Ku bi Allah a cikin abin da ya umurce ku da shi da abin da ya hane ku daga gare shi. "Ku sani wadanda kawai suke jin tsoron Allah daga cikin bayinsa sune Malamai." Daga nan ta ci gaba da cewa:

"Ya ku mutane ku sani ni fa ce Fatima. babana kuma shi ne Muhammad. Ina fada karshe da kuma farko. Ba ina fadar abin da nake fada bane a kan wauta, kuma ba ina aikata abin da nake aikatawa bane a bisa zalunci da danniya. 'Lallai ne hakika Manzo ya zo maku daga cikinku, abin da kuka wahala da shi mai nauyi ne a kansa, mai kwadayi ne gare ku, ga muminai kuwa ntai tausayi ne mai jin kai.' Idan har kuka danganta shi kuka bawanar da shi za ku same shi Babana ne ba na matayenku ba. Kuma dan uwan dan baffana ne ba na mazajenku ba. Lallai. madalla da wanda ake dangatawa gare shi. Ya kuwa isar da manzaaei yana mai bawanar da gargadi mai karkacewa daga tafarkm mushinkai. mai sarar kashin bayansu. mai kame mafitar numfashinsu. mai kira zuwa ga tafarkin Ubangijinsa "tare cla hikima da kyakkyawan wa'azi- " Yana karya gumaka yana surmiyar da manayan kafirai ta kansu "har rundunursu ta tarwatse sukajuya bayct," har dare ya gushe daga way ewar garinsa. gaskiya ta bawana daga tsantsar ta. shugaban addini ya sami lkon magana. sautin shaidanu ya takura. mabiya munafunci suka durkusa. kulle-kullen kafirci da na rarraba suka tarwatse. kuka yi furuci da kalmar lkhlasi a cikin jamaar da sukc daga farare marasa girman ciki (masu yawan azumi da nisantar haram). "kuma kuka kasance a kctn gefen ramin wuta," kuka kasance faro-faron mai jin kishirwa. kuka kasance farautar mai jin yunwa. kuka kasance kyankyashen yuita ga mabukacinsa mai gagagwa. kuka kasance matakar dugadugai. kuka kasance kuna shan gurbataccen ruwa kuna cin busashiyar fata da ganyaye, kuka kasance kaskantattu wulakantattu. "Kunct tsoron kada mutane daga gefenku su mantaye ku." Sai Allah mai girma da daukaka ya tsamar da ku da Babana Muhammad bayan ya hadu da makirce-makirce manya da kanana. Bayan an jarabce sbi da gwarazan mazaje da kurayen Larabawa da tsagerun Yahudu da Nasara, "a duk lokacin da suka hura wuta ga yaki saiAllah yabuce ta," kowane kahon shaidan ya leko ko wata bakar macijiya daga cikin mushrikai ta bude bakinta sai ya jefa dan uwansa a cikin kuryar bakinta, ba ya dawowa har sai ya tattaka kunnuwanta da tafin kafarsa ya buce wutarta datakobinsa 'mashawuya' domin zatin Allah, mai jihadi a cikin umurnin Allah, mukasanci ga Manzon Allah, shugaba a cikin waliwan Allah, mai damara mai nasiha, mai kokari mai wahala, ku kuwa kuna cikin jin dadi daga rayuwa, kuna masu shakatawa da ni'imtuwa, kuma kuna amintattu, kuna jiran aukuwar masifu akanmu, kuna ta sauraren labarin halakarmu, kuna jinkirin fitowa a wajen fito-na-fito. kuna gudu daga yaki. A lokacin da Allah ya zabar ma Annabinsa (SAW) gidan Annabawansa ya zaba masa makomar tsarkakansa, sai kayar munafiinci ta bawana a cikinku, rigar addini ta tozarta, takurarren batattu ya sami iko. wanda ba a san da zamansa daga cikin yyulakantattu ba. ya yi fice. shugaban masu batarwa ya bawana ya yi ginnan kai a cikin huaiminku. Shaidan ya leko da kansa daga mabuyarsa yana tnai kira gare ku. sai kuwa ya same ku masu karbawa ga kiransa. kuna kiyaye yaudarar da ke cikinsa. sannan ya kutsa a cikinku sai ya same ku masu saukin juyawa. ya fiisata ku sai ya same ku masu fushi. sai kuka yi huda (alama) ga rakumin da ba naku ba. kuka gangara mashayar da ba taku ba Wannan duk ya fam a kankanen lokaci tun ciwon (rabuwa da shi) yana da radadinsa. tun raunin bai fara kamewa ba. tun Manzon ba a rufe shi ba. kuka yi gaggawa kuka nya tsoron titina "ku saurara a cikin  a cikin fitina sukafada, kunta lallai jahannama ntai kewayewa ce da kafirai." Saboda haka ya nisanta daga gare kuf Yaya aka yi ne har kuka aikata haka9 Har zuwa ina ne aka juyar da ku? Bayan ga littafin Allah a gaba gare ku. al'amuransa a karara suke. hukunce-hukuncensa a bawane sukc. alamominsa masu haske ne. gargadmsa mabawani ne. umarninsa a sarari suke. Kuka bar shi a bayan bayanku. ko kuna juya masa baya domin kuna kyamarsa ne° iCo kuwa kuna hukunci da waninsa ne'.' kai tir da canjin azzalumai! "Wanda duk ya rungumi wani addinin da ba na Musulunci ba ba za a karba daga gare shi ba, kuma shi a ranar lahira yana cikin tababbu. "

"Daga nan sai ba ku tsaya bata loKaci ba sai uan natsuwar jama'arta, gwargwadon yadda jan akalarta za ta yi sauki gare ku, sannan kuka fara hura wutarta, kuna rura garwashinta, kuna amsa kiraye-kirayen Shaidan batacce, kuna buce hasken addini mabawani. kuna rusa sunnonin Annabi tsarkakakke kuna labewa da guzuma kuna harbin karsana, kuna shirya makirci da yaudara ga Ahlinsa da 'ya'yayensa a boye; muna ta hakuri a kan cutarwarku kamar hakuri a kan sarar adduna da sukar tsinin mashi a kan kashin baya.

"A yanzu kune kuke riya cewa babu gado gare ni? "Ko kuwa suna neman hukundn jahiliwa ne? Waneneyafi Allah kyawon hukunci ga mutane masu sakankancewa?" Ko ba ku sani bane? Lallai ya bawana gae ku kamar bawananniyar rana cewa nd din nan diyarsa ce. Ya ku musulmi! Ashe yanzu har a rinjaye ni a kan gadona? Ya kai dan Baban Kuhafa! A cikin littafin Allah kana gadon babanka amma ni ba ni gadon babana? "Lallai ka zo da al'amari mai girma!! Ko a kan hujja kuka bar littafin Allah kuka jefar da shi a bayan bayanku9 A lokacin da yake cewa "kuma Sulaiman ya gaji Dawud." Kuma ya fada a cikin abin da ya bawanar da kissarsa daga labarin Yahaya dan Zakanwa (AS) a lokacin da yake cewa: "Kayi mani baiwar mataimaki daga wurinkaya gaje ni kumayayigado daga ahalin gidan Yakub." Kuma ya ce "kuma ma'abuta dangane sashensu sun fi cancanta da sashe a cikin littafw Allah." Ya kuma ce "Allah yana yi maku wasiyya a cikin ya'yayenku namiji yana da misalin kason mata biyu." Kuma ya ce "Idan ya bar alheri, wasiyya domin mahaifa da makusanta da abin da aka sani wajabce ga masu takawa (tsoron Allah)," kuka riya cewa babu wani rabo gare ni kuma babu wani gado daga Babana! Kuma babu dangantaka a tsakaninmu! Ko Allah ya kebance ku da wata ayar da ya fitar da Babana daga gare ta ne? Ko kuna cewa masu bambancin addini ba su gadon junansu ne Ashe ni da Babana ba mu kasance ahalin addini guda ba? Ko kuwa kune kuka fi Babana da dan Baffana sanin khasin' Alkur'ani da 'aminsa .

"Tunda dai haka ne. to ga ta nan gaba gare ka da akalarta da sirdinta za ta hadu da kai a ranar tashinka. Kai madalla da niai hukunci.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 next