Tarihin Fatima Zahra [a.s]



Wata rana Manzo ya ziyarci Nana (AS) sai ya ce mata "Ni kam ina so ki dawo kusa da ni. ga ni ga ki." Sai ta ce masa 'Ka yi wa Harisu Ibn Nu'uman magana don shi ya rage mai gida kusa da kai." Sai Manzo ya ce mata mun tambaye shi ba sau daya ba, ni yanzu ina jin kunyar in tambaye shi."

Lokacin da Harisu Ibn Nu'uman ya ji wannan labarin. sai ya zo gurin Manzo yana cewa: "Ya Manzon Allah labari ya iso gare ni cewa kana so ka dawo da Fatima kusa da kai. To wannan gidan nawa ne mallakata ne. Da ni da dukiyata duk mallakarka ne ya Manzon Allah. Wallahi abin da ka amsa shi ya fi soyTiyya a gare ni fiye da abin da ke hannuna." Sai Manzo ya ce "Gaskiya kake fada. mun gode. Allah ya sanya albarka."

Daga nan sai Imam da Nana (AS) suka komo makwabtan Manzo. makwabtan masallacin Manzo. Akwai sad da Manzo ya sa aka toshe duk kofofin shiga masallacin banda nasa da na Imam (AS). Gidan Fatima (AS) da Imam (AS) shi ne fiyayyen gida a doron kasa baya-ga na Mahaifinta. Kusancin gidanta da na mahaifinta ya yi kama da kusancinta da nasa.

An ruwaito cewa: Bayan komawarta kusa da Manzo. yakan ziyarce ta dare da rana cikin kowane lokaci. Su ma sukan ziyarce shi dare da rana cikin kowane lokaci. Babu wani shamaki ko mai iso tsakaninsu da Manzo.

•An ruwato wata rana Manzo yana zaune tare da A'isha a gefen gado. sai Imam Aliyu (AS) ya yi sallama ya shigo Sai Manzo ya buda masa tsakiyarsu a kai ya zauna. Bayan ya zauna sai A'isha ta ce "Ya Manzon Allah yaya zai shiga tsakanina da kai?y Sai Manzo ya ce 'Wannan dan’uwanka ne. surukina. wasiyyina. sannan Allah ya sanya zuriyata su fito daga gadon bayansa. Don haka ba mai shiga tsakanina da shi."

An ruwaito daga Saubani yana cewa: Manzo in zai yi tafiya gidan da yake shiga karshe shi ne gidan Fatima.sannan in ya dawo gidan da yake fara shiga shi ne gidan Fatima. Yakan yi haka ne saboda son da yake mata, da kuma bayyana ma duniya matsayinta da falalarta. An sha tambayar Abdullahi Ibn Umar game da Imam Aliyu (AS), ba abin da yake cewa sai dai ya ce: Ga gidan Manzo ga gidan Aliyu. Wannan ya isa ka gane matsayin Aliyu.

Wata rana an yi tambaya game da matsayin Imam a masallaci, sai Ibn Umar ya ce: "Babu wani gida damfare da masallacin Manzo in banda gidan Aliyu. Wannan ya ishe ku ku gane ko wanene Aliyu."

An ruwaito Ibn Abbas yana cewa: Aliyu makwabcin Manzn Allah ne, masoyinsa ne, makusancinsa ne, shi bako ne mai girma a dakin Allah. Allah shi ke lura da shi. Kai ka ce kodayaushe Allah yana son kusanci ne tare da shi:

1. An haife shi cikin dakin Allah (Kaaba), duk duniya babu wanda
aka taba yi wa haka.

2. Ya rayu cikin dakin Allah (masallacin Manzo don sai ya bi ta ciki
kafin ya shiga gidansa) bayan Manzo ya toshe kofar kowa da
kowa.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 next