Tarihin Fatima Zahra [a.s]



"Daga nan kuma sai ga Baban Hasan, Aliyu Ibn Abi Talib ya shigo ya yi min sallama na amsa masa. Sai ya ce : Ya Fatima ina jin kamshi mai dadi kamar kamshin dan’uwanka, dan Ammina. Manzon Allah." Sai na ce na'am shi ne tare da 'ya'yankacikin bargo. Sai ya nufi inda suke. Sai ya yi sallama. yana cewa: ' Ya Manzon Allah ka yi min izmi in kasance taie da ku cikin bargon." Sai Manzo ya amsa masa, yana cewa. 'Na yi maka izini ya dan’uwanka, Khalifana. Sahibina. mai rikon tutata' Sai ya shiga tare da su. Bayan nan sai na zo gurinsu sai na yi sallama. Ina mai cewa ya Babana. ya Manzon Allah ka yi min izini in shigo tare da ku. Sai ya amsa. yana mai cewa 'Na yi maki izini ya diyata.bangaren jikina

"Lokacin da suka shiga dukkansu. sai Manzo ya fito da hannunsa na dama ya daga sama yana mai cewa: " Ya Ubangiji wadannan su ne iyalan gidana. zababbuna. Jikinsu jikina ne. jininsu jinina ne. yana min radadi duk abin da ya yi musu radadi. Ni mai yakin duk wanda ya yakc su 'ie. mai aminci ga duk wanda ya amince musu. abokin gaban duk wanda ya yi gaba da su ne. Salatinka. albarkanka. rahmarka. gafararka. da yardarka a gare ni da su baki daya. Sannan ka tafiyar musu da dauda. ka tsarkake su tsarkakewa.'

A wannan lokaci sai Allah Mabuyyayi da daukaka ya ce: Ya Mala ikuna. ya mazauna sammaina. ban halicci wata- sama ginanna ba. ko kasa shimfidaddiya. ko wani wata mai haskc ko rana mai haskawa. ko wata duniya mai kewayawa. ko tekn mai gudana sai don kaunar wadannan mutum biyar din cikin mayafi."

"Sai Jibrilu ya ce " Ya Ubangijina su wanene cikin wannan rnayafin?" Sai Allah Mabuwayi da daukaka ya ce "Sune iyalan gidan Annabi. taskar manzanci. su ne: Fatima. Mahaifinta. tnijinta da 'ya'yanta! Sai Jibrilu ya ce ' Ya Ubangijina ka yi min izini in sauko kasa in kasance na shidansu." Sai Allah Mabuwayi da daukaka ya ce 'Na yi maka izini

"Sai Jibrilu (as) ya sauko kasa ya ce 'Assalamu alaika ya rasulullah! Madaukakin Madaukaka yana yi maka sallama. yana kebantarka da  gaisuwa da karimci, yana fada game da kai, yana cewa 'Na rantse da Buwayata da daukakata. ban halicci wata sama ginanna ba. ko kasa shimfidaddiya, ko wani wata mai haske, ko rana mai haskakawa, ko wata duniya mai kewayawa, ko teku mai gudana, sai dominku. Hakika ya yi min (Allah) izini in shigo cikin wannan mayafin tare da ku, kai ma ka yi min izini?"

"Sai Manzo ya amsa yana mai cewa: 'Na yi maka izini ya Jibrilu Amintacce gun wahayi." Sai Jibrilu (as) ya shiga yana mai cewa: "Allah ya yi min wahayi  zuwa gare ka: Yana mai cewa: 'Lallai Allah yana nufin ya tafiyar da dauda ne daga gare ku Ahlul bait, kuma ya tsarkake ku tsarkakewa.'

"Sai Aliyu Ibn Abi Talib ya ce ' Ya Manzon Allah ka ba ni labarin falalar wannan haduwar tamu a wajen Allah." Sai Manzo ya ce mishi: 'Na rantse da wanda ya aiko ni da gaskiya. ya daukaka ni da sakonsa. babu wani taro a cikin tarukan duniya wanda ciki akwai shi’armu. masoyanmu da za a ambaci wannan haduwar tamu face an saukar musu da rahma. sannan Mala'iku su kewaye su' Sai Aliyu (as) ya ce 'Na rantse da Ubangjin Ka'aba lallai mun rabauta shrarmu sun rabauta. Sai Manzo ya kuma cewa "Na rantsc da wanda ya aiko ni da gaskiya. ya daukaka ni da sakonsa. babu wani taro cikin tarurrukan duniya wanda ciki akwai shi’armu. masoyanmu da za a ambaci wannan haduwa tamu face Allah (swt) ya yaye ma duk wani mai bakin ciki bakin cikinsa Babu wani mai neman biyan bukata face Allah (swt) ya biya masa bukatarsa' Sai Aliyu (as) ya ce: Lallai wallahi mun rabauta. mun azurta Haka shi’armu sun rabauta sun azurta duniya da lahira

(5). An niwato daga Imam Sadik (AS) yana cewa: Fatima (AS) ya ce
lokacin da aka saukar da ayar da Allah yake cewa "Kada ku dinga kiran ,Manzo kamar yadda kuke kiran junanku,." sai ta ce "Na ji tsoron in
kira shi da sunan 'Ya babana' Sau biyu ko sau uku ina kiran sa: "Ya
Rasulullah." amma ba ya amsa min. Sai ya ce Ya Fatima. Wannan ayar ba a kanki aka saukar ba ko iyalanki. Ke daga gare ni kike. ni ma daga gare ki nake. An saukar da ita ne kan wawayen Kuraishawa. Ki dinga kira na 'Ya Babana." shi ya fi soyuwa a gare ni." '

(6) An ruwaito daga A'isha tana cewa: Ban taba ganin wanda muryarsa. zancensa. ya yi kama da na Manzo ba kamar Fatima. Idan ya hango tana zuwa yakan tarbe ta. ya sumbanci hannunta. va.yi mata barka da zuwa. Sannan ya zaunar da ita inda yake zaune. Ita ma in ta gan shi yana zuwa takan tarbe shi. ta sumbanci hannunsa tana mai mishi barka da zuwa.

(7). Bazalul Harwi ya tambayi Hasan Ibn Ruhu cewa 'ya'yan Manzo mata nawa ne'} Sai ya ce su hudu ne. Sai ya ce wacce ce ta fi daukaka cikinsu, Sai ya ce Fatima. Sai ya ce me ya sa haka alhali lta ce karamar cikinsu? Sai ya ce hakan ya faru ne saboda abubuwa biyu. wadanda ta kebanta da su: (a) Ita ce wacce ta gaji Manzon Allah. (b) Zuriyarsa ta tsatsonta za su fito.Allah bai kebance ta da wannan falalar ba. sai don ikilasinta wajen niyya.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 next