Tarihin Fatima Zahra [a.s]



Ashirin ga Jumada sani muka sami Fatima Musamman ranarki har da watan duka dukka ma Ko da bako ne ya shigo birninmu ma Ya san lallai a garin ga ana son Fatima.

 

BAYANIN DAUKAR CIKIN FATIMA (as)

Ya zo a Biharul Anwar na Allama Majalisi (ra) cewa: Wata rana Manzo yana zaune sai Malaika Jibrilu ya zo masa. Sai ya ce "Ya Muhammad, Madaukakin Madaukaka (Allah) yana gaishe ka. kuma yana maka umurni da ka nisanci Nana khadija (as) har tsawon kwana arba'in."' Sai Manzo ya kira Ammar Ibn Yasir (ra) ya aike shi wnrin Nana Khadija (as). a kan ya gaya mata: "Ya Khadija kada ki yi zaton yankewata daga gare ki hijira ce ko juya baya. a'a sai dai Ubangijina ne Mabuwayi ya umurce ni don ya zartar da al amannsa kada ki yi zaton komai sai alkhain. ldan darc ya y 1 ki kulle kofa. ki tafi ga makwancinki. ni kuma ina nan gidan Fatima binti Asad.

Manzo ya kasance cikin gidan Fatima binti Asad har kwana arba'in. yana azumi da rana. yana kuma tahajjud da daddare. Bayan cika kwana arba'in sai Mala ika Jibrilu ya zo masa yana mai shaida masa cewa ya koma zuwa ga Khadija (as). ya kuma zo masa da abinci inn na Aljanna don ya yi buda baki da shi Bayan buda baki. sai ya mike don yin salla. sai Jibrilu ya fuskanto shi yana mai shaida masa cewa kada ya yi wannan sallar har sai ya je dakin Nana Khadija domin Allah (swt) yana so ya halitta a tsakaninsu cikin wannan daren zuriya mai tsarki.

Ga wata ruwayar kuwa ita ce: Sad da Manzo ya yi Israi ya ciwo wannan abincin na Aljanna aka sami cikin Nana Fatima (as). An niwaito daga Ibn Abbas yana cewa: A'isha matar Manzo ta ga Manzo yana sumbantar Nana Fatima (as) sai ta ce kana son ta ne ya Rasulullah? Sai ya ce "Wallahi da kin san son da nike mata a zuciyata. da ke ma kin kara son ta  Lokacin da aka yi Isra'i da ni zuyya sama ta hudu. (har inda yakc cewa: sai naga fure mai kyau kamshinsa wane almiski, dandanonsa kuwa wane zuma, sai na tsinka na ci, sai ya' zama maniyyi a gadon bayana.Lokacin da na sauko kasa sai ya koma mahaifar Khadija aka haifi Fatima.Fatima matar Aljanna. ce a surar 'yan' Adam. In na ji begen Aljanna nakan sumbance ta."

Mustapha Gadon Kaya yana cewa a wake:

Sanda Manzo yai Isra'i ya ce na ga wata mace mai jin sarauta,

Ta sa kambun sarauta Hurul'in sune khadimanta,

Ya ce wacece wancan aka ce diyarka Nana,



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 next