Tarihin Fatima Zahra [a.s]



Allah (swt) yana cewa: "Lallai wadanda suka yi kokari a tafarkinmu za mu shiryar cla su hanyoyinmu." Kafin bayA anar Manzo. Nana Khadija (as) ta yi aure har sau biyu a farkon kuruciyarta. Da farko ta auri Atik bin A'id bin Abdullahi, daya daga cikin 'yan kasuwan Makka. Ya rasu bayan auren. ba da jimawa ba. Ga wata ruwayar an ce ba su yi kwanan aure tare ba. Nana Khadija (as) ne ta gaje dukiyarsa gami da na Mahaifinta wanda ta gada.

Bayan haka kuma sai ta auri Abi-Halala (Hindu bin Banar). yana daga cikin samarin "yan kasuwan Makka masujari da kadarori. Shi ma bai jima a duniya sosai ba. sai ya rasu. ya bar mata gado mai yawa da kadarori. wanda wannan ya sa dukiyar ta yi yawan da tilas a lissafa ta cikin manyan masu kudin Makka. Ga wata ruwaya an ce sun haihu da shi diya guda daya. har ma bayan da Manzo ya bayyana ta yi imani da shi. Ga wata ruwayar kuma an ce ba su haihu da shi ba.7

Abin da muka atnbata game da auren Nana Khadija (AS) ga Atik bin A'id bin Abdullahi a Abi Halala (Hindu bin Banar) shi ne abin da ya fi shahara a mafi yawa daga ruwayoyin sunni.

Amma abin da ya fi inganci a kan wannan na daga ruwayoyin kadan daga cikin manyan mlaman sunni da kuma jumhurin manyan malaman shi’a su ne: Nana Khadija ba t taba yin wani aure ba gabanin ta auri Manzon Allah (SAAW). Manzo ya aure ta ne tana budurwa ba tare da ta taba yin wani aure ba a rayuyyarta.

An ruKaito daga Ibn Shar Ashubi yana cewa: Ahmad Alballaci da Abu Kasim Alkufi sun ruwaito, da kuma Almurtada cikin Asshafi da Abu Ja afar cikin Talkis suna cewa: Lallai Manzon Allah (SAAW) ya aure ta ne (Khadija) tana budurwa.

Wannan hadisin da wadanda suka yi kama da shi suna da yawan gaske na daga ruwayoym sunni da shi a ba za mu tsawaiia a Kai oa. sai dai mai karatuyana iya cigaba da bincikawa cikin littafan da muka ambata

Nana Khadija (as) kasantuwar tana da jan mai karfi sai ta fada hanyar kasuwanci, ta biyan amintattun mutane suna zuwa suna yo mata fatauci a gurare daban-daban suna kawowa. ita kuma tana saidawa. tana samun riba tana taimakon jama'a. Ya zo a cikin "Biharul Anwar" cewa Nana Khadija (as) tana da rakuma dubu takwas da dukiyoyi a sassa na kasashe daban-daban. ana mata kasuwanci. kamar Misra. Habasha. Sham da sauransu. Nana Khadija (as) ta tara dukiya mai yawan gaske. Mafiya yawa daga cikin manyan masu kudi da masu mulki sun neme ta da aure. to amma ba ta amsa musu ba, don ta riga ta yi kwalliya da tufafin nan na jiran Annabin karshe da taimaka masa mutukar rayuwarta.

Manzo ya kasance yana tare da Amminsa (Abu Dalib) yana taya shi wasu aikace-aikace. wanda ya hada har da siye da siyarwa. Ga wata ruwayar sai ya shawarci Manzo akan ko zai yarda ya yi wa Nana Khadija Fatauci tana biyan shi, ko sa samu :yan kudi don rage wadansu yan wahalhalun. Yana mai cewa Lallai Khadija za ta yi murna sosai don tana son mutum mai gaskiya da rikon aniana. na kuma tabbatar kana da gaskiya da rikon amana. don haka ake maka lakabi da Alamin

Ga wata ruw ayar kuma shi ne. kamar yadda muka fada baya cewa zuciyarta ta damfaru da son wannan Annabin karshen. Daga nan sai ta yi tunanin ko shi ne wannan Muhamniadun da kowa yake ba da labann kyawawan dabi unsa. don haka sai ta yi nufin ta jarraba shi. Sai ta aikc masa a kan ya zo ya yi mata fatauci ta biya shi. shi kuma Manzo ya amsa mata.

Bayan ta hada shi da bawanta (Maisara) sun tafi Sham sun dau o sai aka sami riba mai yawa. wanda ba a taba samun irinsa ba Kuma Maisara ya ba ta labann abin da ya gani na mu'ujizozi ga Manzo yayin tafiyarsu da dawowarsu, kamar yadda girgije ya yi musu inwada sauransu. ko da Nana Khadija ta ji haka, sai ta samu yakinin wannan shi ne zai zama Annabin karshe. Wani aikin sai masu shi. ta gaskata Allah kuma Allah (swt) ya gaskata ta.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 next