Tarihin Fatima Zahra [a.s]



 

(g) MARDIYYAH (as)

Kasantuwar mutum cikin wadanda Allah (swt) ya'yarda da su shi ne mafi girman daraja. Wanda Allah (swt) ya yarda da ayyukansa baki daya. komai kankantar aikin da ya yi Allah (swt) zai yarda da shi. Nana (as) tana cikin wadanda Allah (swt) ya yarda da su, don haka ake mata lakabi da Mardiyya. Ta yarda da duk abin da Allah (swt) ya saukar mata na wahalhalu. shi kuma Allah (swt) ya yarda da duk abin da ta aikata.

 

(h) MUHADDATHA (as)

MUHADDATHA: Ma'ana a nan shi ne wacce Mala'iku suke zance ko hira da ita. Ya zo a wurare daban-daban. inda Mala'iku suke zance da Annabawa ko Manzanni da kuma wadanda ba Annabawa ba kamar Maryam (as). Ummi Musa (as). Saratu matar Annabi Ibrahim (as) da sauran su. Mala lku sun kasance sukan zo gidan Nana (as) da rana domin kawai su yi mata aiki. An ruwaito daga Zaid Ibn Aliyu (as) cewa yaji Imam Bakir yana c'ewa an ambaci Fatima da Muhaddatha ne saboda Malai kun sama sukan sauko su yi yekuwa kamar yadda suke yiwa Maryam binti Imran (as) suna cewa "Ya Fatima lallai Allah (swt) ya zabe ki ya tsarkake ki ya kuma fifita ki a kan sauran matan duniya baki daya."

Nana (as) ta rayu bayan wafatin Mahaifinta da kwana 75. Ta kasance cikin bakin cikin rabuwa da Mahaifinta A wannan lokacin Mala ika Jibrilu (as) yakan zo gurinta kullum don ya dadada mata. ya kuma ba ta labarin Mahaifinta da halin da yake ciki tia niima. Yakan kuma ba ta labarin abm da zai faru bayan w afatinta har zuwa tashm kiyama. shi kuma Imam Alnai (as) yana rubutawa. To wannan shi ne ake kira da MUSHAFIN FATIMA (as).

 

(i) ZAHARA'U (as)

An ruwaito daga fbn Abbas yana cewa "Na ji Manzo yana cewa: Lallai Diyata Fatima ita ce Shugabar matan duniya tun daga farkonsu har zuwa karshensu Lallai ita tsoka ce daga gare ni. lallai ita ce abin begena. lallai ita kyyanciyar hankalina ce. lallai ita ce ma Ruhina wanda ke cikin kirjina Ita macen Aljanna ce a suran dan Adam. A duk lokacin da ta mikc gaba ga Ubangijinta mai girma da daukaka don ibada sai haskenta ya bayyana ga Mala" ikiin sama kamar yadda taurari suke bayyana ga mutanen duniya."



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 next