Tarihin Fatima Zahra [a.s]



Nasabar Nana Fatima a.s zuwa ga Annabi Ibrahim

Nana Fatima Binti Muhammad (saww), Ibn Abdullahi. Ibn Abdul Mutailib. Ibn Hashim, Ibn Abdulmanaf. Ibn Kusaiyi, Ibn Kilab; Ibn Marra, Ibn Ka'ab, Ibn Luayyi, Ibn Galib. Ibn Fihir, Ibn Malik, Ibn Nasar, Ibn Kinana, Ibn

Kuzaima, Ibn Mudrik, Ibn Ilyas, Ibn Mudar, Ibn Nizar. Ibn Ma'ad. Ibn Adnan, Ibn Udd

(Udad), Ibn Muqayvyvam, Ibn Nahur, Ibn Tayrah, Ibn Ya'rub, Ibn Yashjub. Ibn Nabit.Ibn Isma'il (as).

Dangane da bayanin salsalarta za mu faro ne daga Adnan. don koyi da hadisin Manzo inda yake cewa idan kuka danganta ni ko kuka nasabta ni zuwa ga Adnan sai ku tsaya." Asalin Manzon Allah (swt) haske ne wanda yake fita daga mahaifa zuwa mahaifa na daga Annabawa. Manzanni. da Waliyyai har zuwa lokacin da Amina (as) ta dauki cikinsa ta haife shi. kamar yadda za mu dan yi bayani a gaba.

Bayan haihuw arsa. kafin ya bar duniya wannan hasken. wanda Allah (swt) ya ambace shi da fitila mai haskaka zukatan muminai ta wajen nuna musu shiriya. ya ci gaba da gudana ta hanyar ya yanta Imam Hasan a Imam Husain (as) dajikokinta (Imamai) bayan mijinta Imam Aliyu (as)

Adnan Ibn Udd: Sunan mahaifiyarsa Balha'u. An haife shi a nan cikin garin Makka a shekara ta 130 kafin bayyanar Annabi Isa (as).

Lokacin da yake yaro an ji daga cikin bokayen wannan lokacin wata tana cewa: Wannan yaron a cikin tsatsonsa za a haifi wani mutum wanda zai zama shugaba ga Aljannu da mutane. Ya kasance kyakkyawan mutum mai shaja’a, Saboda bayanin da wannan bokar ta yi sai masu hassada suka tare shi su 80 a dokar daji don su kashe shi. Bayan ya kashe da yawa daga cikinsu sai ya gudu ya zuwa wani gindin dutse. Ko da suka bi shi sai dutsen ya yi tsawa. sai suka mutu gaba dayansu. Wannan ya bayyanar da Muujizar annabta wacce take gadon bayansa.

Lokacin da ya kai shekaru 30 zuwa 40. sai mutanensa suka kira shi a kan ya zama musu shugaba. har ya zama shi ke shugabancin kabilun da ke Makka da kewayenta baki daya.22Bayan wannan lokacin sai Bakti Nassar ya zo ya ci da yaki, suka tafi watsu sassa daban-daban Shi Adnan da wasu Sahabbansa. suka tafi Yaman suka zauna har Allah ya yi masa rasuwa.

 

MA'AD IBN ADNAN: An haife shi ne a shekara ta 97 kafin zuwan Annabi Isa (as). Bayan mutuwan Bakti-Nasar, sai Kabilun Larabawa suka aike masa a kan ya zo ya zama shugaba a gare su, saboda alamomin da suka gani tare da shi na shugabanci. Watau wannan haske na annabta.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 next