Tarihin Fatima Zahra [a.s]



Mai karatu yana iya ganin cewa wannan har yau shi ne wanda yake a cikin shari'ar Musulunci wanda wannan babbar ishara ce ga cewa duk cikan kakannin Imam Husain (as) babu wanda ya taba rayoiwa ba inn ta Musulunci ba. tun daga na farkonsu har ya zuwa na karshensu.

Allama Majlisi ya niwaito yana cewa: Lokacin da abin  da yake

uwa ma mazaje na girma ya zo ma Abdullahi, sai ya zama duk wata

mace mai isa takan bijiro da kanta da dukiyoyinta'baki daya gare shi don

ya aure ta. saboda wannan hasken da yake daukc da shi naManzonAllah(saww).

Ya kasance a zamaninsa babu wani 'wanda ya-kai shi kyau. kamala da haiba. Sdan da rana ya wuce cikin Jamaa. babu abin da za su dinga ji sai kamshin Almiski. Idan kuma da daddarc ne sai hasken tiiskarsa ya dingahaskakeko'inadaina. harsunayi masalakabi da'Titilar Harami".

Ibn ishaq ya mwaito cikin littafin tarihinsa yana cewa: Wata rana Abdullahi suna tafiya tare da mahaifinsa za su gun Wahab Ibn Abdulmanaf Ibn Zuhra. wanda shi ne shugaban Banu Zuhra, sai wata budurwa daga cikin matan Banu Sa'ad. ta ce masa "Da za ka yarda ka aure in da na ba ka rakuma adadin rakuman da aka fanshe ka da su." Sai ya ce mata: "Ni tnatareda tnahaifina. ki.yi hakuri babu wani hukunci da zan yanke a kashin kaina."

Lokacin da suka isa ga Wahab Ibn Abdulmanaf sai ya aurar wa Abdullahi da diyarsa wacce ake kira da sunan Aminatu Binti Wahab Ibn Abdulmanaf Ibn Zuhar Ibn Kilab Ibn Murra.

Bayan nan sai ta sami cikin Muhammad (saww), ta haife shi. Shi kuma ya haifi Fatima (As).

Ba wani ne Mahaifin Nana Fatima (as) ba illa Manzon Allah Annabi Muhammad Ibn Abdullahi (saw) wanda sanin shi ba mai boyuwa bane ga dukkan halitta baki daya. Domin Allah (swt) ya gwama saninsa da nasa ya kintsa shi ga dukan halitta baki daya. Ya zo a cikin Ashifa cewa idan Manzon (saw) ya fita bayan garin Makka, bishiyoyi da duwatsu sukan yi masa sallama suna masu girmamawa zuwa gare shi. alhali kuma girjije yana masa inuwa. Sannan kuma wata rana Manzo (saw) ya kira wani Balaraben kauye a kan ya musulunta. sai Balaraben kauyen ya saki wani damo da ke hannunsa ya ce ba zai yi imani ba, sai wannan damon ya yi wa Manzo shaida. Sai wannan damon kuwa ya budi baki ya ce ya shaida babu abin bauta da gaskiya sai Allah. Annabi Muhammad Manzonsa ne kuma bawansa ne. Sai wannan Balaraben ya musulunta yana mamaki, har ya ce da Manzo ya ba shi izini ya yi masa sujuda don girmamwa. sai Manzo ya ce a a Allah (swt) kawai ake wa sujuda. Ya ce to ya bar shi ya sumbanci hannunsa don girmamaw a sai Manzo ya ba shi hannunsa ya sumbanta.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 next