Tarihin Fatima Zahra [a.s]



Sannan sai ya ci gaba da cewa: "Sai Manzo ya ce mata 'Ya diyata AHah shi ne Khalifana a gare ku kuma shine mafi kyawun khalifanci. Na rantse da wanda ya tayar da ni da gaskiya, hakika Al'arshin Allah da Mala'i kun dake kewaye da shi, da sama da kasa da abin da ke tsakanin su, sun koka da kukanki. Ya Fatima na rantse da wanda ya aiko ni da gaskiya, an haramta wa dukkan halittu shiga Aljanna baki daya har sai kin shiga. Ke ce farkon halittar da zai shiga Aljanna bayana cikin kwalliya da annashuwa. Ya Fatima kin ji dadinki. Na rantse da wanda ya aiko ni da gaskiya, Jahannama za ta yi kugi, kugi sosai, wanda babu wani Mala'ika mukarrabi ko Manzo face ya suma, sai a yi kira zuwa gare ta a ce AL JABBAR ya ce ki natsu da izzarsa. Har sai Fatima ta shiga Aljanna "babu wani tsoro tare da ita. Na rantse da wanda ya aiko ni da gaskiya, za ki shiga Aljanna Hasan na hannunki na dama Husain na hannunki na hagu. Za ku zauna a Aljanna mafi daukaka gaba ga Ubangiji. Sannan tutar yabo-yana hannun Aliyu Ibn Abi Talib. Na rantse da wanda ya aiko ni da gaskiya. sai na yi shan'a da duk wanda ya zalunce ki gobe kiyama a gaban Allah!!".

Ga wata ruwayar kuwa: "Manzo ya kira Imam Aliyu. Fatima. Hasan da Husaini (as) sannan ya ce duk sauran mutane su fita. Ummi Salma ta tsaya a bakin kofa kar ta bar wani ya shigo. Sai ya ce ma Aliyu matso kusa. sai ya kama hannun Fatima (as) ya daura a kirjin sa tsawon lokaci. sannan ya kama hannun Aliyu da daya hannunsa. Yana son ya yi magana sai ya kasa. Sai Fatima ta fashe da kuka. kuka sosai. Aliyu, Hasan, Husain duk su ma suka fashe da kuka. Sai Fatima ta ce 'Ya Manzon Allah zuciyata ta gama konewa saboda kuka. Ya Shugaban Manzanru na farkonsu da na karshensu. ya Amintaccen Ubangiji, Manzonsa. Annabinsa. sannan kuma Masoyinsa. wa zai zama uba gare ni bayanka7 Kaskanci ne zai zo min bayanka? Wa zai sanar da ni wahayin Allah da umurninsa?" Sai ta kuma fashewa da kuka da hada kanta da nasa. sai ya sumbance ta. ya daga kansa sama ya dttbe su (Fatima. Aliyu. HasStn. Husain) ya dauki hannun Fatima ya daura a kan hannun Aliyxi ya ce: Ya Baban Hasan ga amanar Allah da Manzonsa Muhammadu a hannunka. ka nemi taimakon Allah da Manzonsa wajen rucewa aon na san za Ka lya. ira. Aiiyu wanani wannan ita ce Shugabar matan Aljanna, na farkonsu da na karshensu Ita ce Maryam Kubra.

Wallahi tun kafin wannan lokacin na rokar mata Allah wannan matsayin, da ku, kuma ya amsa min. Ya Aliyu ka aikata duk abin da ta umurce ka da shi don na umurce ta da abubuwa da yawa, wadanda Mala'ika Jibrilu ya yi umurni da su. Ka sani ya AliyTi ni mai yarda ne da abin da ta yarda da shi, haka su ma Mala'iku da Ubangijina Sai Manzo ya rungume Fatima zuwa gare shi ya sumbanci kanta ya ce: Mahaifmki fansanki ne ya Fatima...

"Hasan da Husaini suna tsotson kafarsa suna kuka. Imam Aliyu ya so ya daga su, sai Manzo ya ce 'kyale su, su shake ni, ni ma in shake su, su yi guzuri da ni, ni ma in yi guzuri da su. Bayana za su hadu da girgiza mai tsanani na gaba da kisa. Ya Allah na ba ka amanarsu." Fatima kuwa tana kuka mai tsanani. hawaye suna ta zubo mata, tana kuka tana cewa: 'Na fanshi ranka da raina, na fanshi rayuwarka da raymya ta!! Ya babana ba ka fada min wata kalma ba, ga shi ma kallon ka alamun mutuwa sun zo gare ka, rabuwa ta zo?" Sai ya ce 'Diyata lallai rabuwa ta zo! Amincin Allah ya tabbata gare ki'

Ga wata ruwayar kuwa, sai ya ce: Za a zalunce ki bayana. za a raunatar da ke bayana. Duk wanda ya cutar da ke ya cutar da ni, wanda ya wulakanta ki ya wulakanta ni. wanda ya yi mu'amala da ke ya yi da ni. wanda ya yanta miki ya yanke min. domin ke daga gare ni kike. ke tsoka ce daga gare ni. ke ruhina da ke cikin jikina ne." Sannan ya ce Ina kai kara gurin Allah ga duk wanda ya cutar da ke daga cikin al'ummata. Bayan nan sai Imam Aliyu ya bawana ma jama'a wafatin Manzo. yana tnai cewa: Allah ya ba ku lada mai yawa don Annabinsa. Hakika Allah ya amshi ransa. Sai jama'a suka mike da kuka. wanda ba a taba yin irinsa a doron kasa ba!!

Lokacin da Nana ta ga Mahaifinta kwance ba ya motsawa sai ta fashe da kuka. tana cewa: "'Ya Babana. wa ya yi kusancinka wajen Ubangiji! Aljannar Firdausi ita ce makomarka! Ga Jirilu nake mika ta"aziwarka! Ya Babana ka amsa kiran Ubangiji!!" Su kuwa Imam Aliyu yana kuka yana cewa "Ya Rasullullah!" Su kuma Hasan da Husaini suna kuka, suna cewa "Ya  kakanmu

Daga nan sai Imam Aliyu ya yi mashi wanka ya sanya masa likkafani sannan aka yi mashi salla. In wannan jama'a sun yi mashi salla, sai wata jama'ar ta zo ta yi mishi nata sallar. Iyalan gidan Manzo suna cikin jama'ar farko da suka fara yi masa salla.

Tun bayan wafatinsa Fatima (as) take kuka ba kakkautawa har suka dawo gida. Matan Madina duk sun taru a gidanta. Farkon maganarta da su shi ne. "'Daga Allah muke kuma gare shi za mu koma! Labarin sama ya yanke mana. Yanzu mutane za su iya tona kasa su mayar da ita kan Manzon Allah?"

An ruwaito daga Imam Baqir (as) yana cewa: "'Ba a taba ganin Fatima ta kuma yin dariya ko wani farin ciki ba bayan wafatin Mahaifinta har ta koma ga Ubangijinta!!!"

An ruwaito daga Imran Ibn Dinar yana cewa: "Fatima ba ta kuma yin dariya ba bayan w afatin Mahaifinta saboda bakin cikin rabuwa da shi har ta koma ga Ubangijinta!!"



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 next