Tarihin Fatima Zahra [a.s]



3. An kashe shi cikin masallaci yana sujuda. Sannan a lebensa akwai
sunan Allah!

An ruwaito daga Anas Ibn Malik yana cewa: Manzon Allah (SAW) ya karanta ayar da Allah (SWT) yake cewa. "Cikin wasu gidaje wadanda Allahyayiizini da a dinga ambatonsa..." Sai wani yamike ya ce "Wane gida ne ya Manzon Allah'" Sai Manzo ya ce "'Gidan Annabwa ne." Sai Abubakar ya mike ya nuna gidan Fatima ya ce "Wancan yana cikinsu?" Sai Manzo ya ce "Na'am yana daga cikin mafificinsu."'

An ruwaito daga Ibn Abbas yana cewa: Wata rana muna zaune tare da Manzo a masallacinsa sai wani ya karanta ayar da Allah (SWT) yake cewa "Cikin wasu gidaje wadnaa Allah ya yi izini da a dinga ambaton sa.." Sai na ce "Wane gida ne ya Manzon Allah?" Sai ya ce "Gidajen Annabawa ne." sai ya yi nuni da gidan Fatima. ya ce yana daga cikinsu.      

Rayuwar Nana Fatima (a.s) A gidan Miji: 

 Nana (AS) ta baro gidan Mahaifinta, gidan Annabta da Manzanci zuwa gidan mijinta gidan Imama, Khalifanci, wasiyanci da wilayanci don zaman aure, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. Mai karatu ba sai ria gaya rtiaka irin zaman da aka'yifea na soyayya. kauna, aminci, 1-ausayi, ibada. ilimantarwa. infaki, dss. Domin Allah bai taba hada aure irin  wannan ba. Da Da mijin da matar duk tarbiyyar Manzon Allah ne ba waninsa ba. Fatima ta San ko Imam. Aliyu, wane ne ta san matsayinsa a wajen Allah da Manzonsa. Tana girmama shi fiye da yadda kowace mace take  gimama  mijinta, Ba ma kawai a matsayin mijinta ba, a'a har ma a matsayin Imaminta!,'Babu wani hakki na Imam AIiy (AS) wanda ba ta ba da shi dari bisa dari ba, har shi da kansa yana cewa Wallahi ban taba bata mata rai ba, koÉ“saba mata. Ita ma ba ta taba bata min rai ba, ,kota (abafaikata! wani abin ki, har Allah (SWT) ya: amshi ranta. Na kasan ce nakan kalli fuskarta sai bakin cikin da damuwa su kwaranye.

!An ruwaitp,daga Imam Bajdr (AS) yana cewa  Fatima ta jibinci al'ainuran gida baki daya, da hannunta take yin sa kuma Imam Aliy  ya jibinci fita waje ya kawo abinci da itace dafawa.Akai kareraki da  da ake yi dangane da wannan  gidan mai alfarma wanda kullum manzo bai iya barci sai yaje Duk sadda  ya yi tafiya ko ya je  ya ki hankalinsa na kan gidan. Yana dawowa ba inda zai nufa sai gidan wai an  sha Samun sabani da rashin jituwa tsakanin maaura^tan.'kamar  in Imam ya ce zai kara aure dss, wannan sam ba gaskiya ba ne. Bayan    Malainai a kai ba don gudun tsayyaitayya, .anipia, mai karatu yana iya bincikawa.

sayyida ta sami'cikin Imam;Hasan (As) tana;da  shekara goma sha biyu duniya. Lokacin da tadauki cikinsa sai hasken fuskarta ya karu kan a kan haskenta Saboda hasken  nan na Imama da ke gadon bayanImam Aliyu (AS) ya dawo cikin mahaifanta.

Wata tafiya  ta bijirowa, Manzo a lokacin da haihuwarta ta karato tajiara!S'ai Manzo ya biya gidan kamar yadda ya saba. Ya yi mata wasiyya"a kan in har an haife shi kada a lullube shi da zane mai fatsi-fatsi. A'cikin watan azumi, azumi ya kai sha biyar, Nana ta dau azumi sai Allah ya kawo mata nakuda, hijira na da shekaru uku. Ta haife shi cikin mafi saukin nakuda ba tare da jini ya diga ba, ko digo! Cikin koshin lafiya. Kamar yadda muka yi bayani baya cewa ita ba ta haila irin na mata ko biki, kullum cikin tsarki take da kusanci zuwa ga Ubangijinta. Ko da ta haife shi ta ci gaba da azuminta.

Asma'u bin Umais ita ce ta yi masa ungozoma. Sai dai ta mance, ko ba ta sani ba game da wasiyyar Manzo na kada a lullube shi da zane mai fatsi-fatsi. A wannan ranar tun daga gidan Imam Aliyu, gidan Manzo har zuwa duk garin Madina kowa da kowa sai farin cikin haihuwar Imam Hasan (AS).

Nana (AS) ta kira Imam a kan ya yi masa suna, sai ya ce ba zai shiga gaban Manzo ba wajen sanya masa suna. Lokacin da Manzo ya dawo sai ya ce a dauko shi, sai ya ga an lullube shi da abin da ya hana. sai ya ce "Ashe ban hane ku ba? Sai ya yi yyurgi da zanen. Ya ce a kawo masa farin zane Aka kawo masa ya lullube Imam Hasan (AS) da shi.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 next