Tarihin Fatima Zahra [a.s]



An haife shi a Madina. kuma a can ya girma garin dangin mahaifiyarsa. Bayan ya girma sai dan uwan mahaifmsa. Mudallib yaje Madina ya taho da shi a kan rakumi. lokacin shi ne shugaban mutanen Makka. Ko da mutanc suka gan shi daukc da yaro sai suka yi zatan ya sayo bayya ne daga Madina. Sai suka kama kiran yaron da sunaAbdul Mutallib. ma'ana bawan Mudallib. Mudallib ya yi musu bayani cewa sunansa Amr. amma ina. Lokacin da AbdulMutallib ya girma. ya zama kowa sai zancensa yake yi saboda kamalarsa. sai Mutallib ya mika masa shugabancin Larabawa. sai ya zama shugabansu.

ABDULLAHI IBN ABDUL MUTALLIB: Sunan mahaifiyarsa Fatima binti Araru. Aii haife shi ne shekara 535 bayan bayyanar Annabi    Isa [a.s] lokacin da aka haife shi bai boyu ga manyan malaman

Yahudawa ba da Nasara, har ma da shahararrun bokayen wannan lokacin. Daga cikin alamar da malaman Yahudu da Nasara suka gane an haifi mahaifin cikamakin Annabawa shi ne bicewar jinin Annabi Yahya (as) wanda yake jikin rigarsa. wacce Yahudawa suka kashe shi yana sanye da lta.

Wannan hasken ana haihuwar shi sai ya koma ya zuwa gare shi duk ya haskake fuskarsa baki daya. Ya kasance tun yana yaro yake ganin abubuwa na ban mamaki da al'ajabi. Shi da kansa yana fada ma mahaifinsa cewa: "Na kasance idan na tafi ya zuwa wani daga cikin duwatsun Makka. sai wani haske ya fito daga fiiskana, ya mika Gabas da yamma sannan ya hade kamar daira sai ya yi sama kamar girgije. sannan ya dinga yi min muwa. yana kare ni daga zafin rana. Sannan kuma daga karshe sai ya kuma dawowa fuskata. Duk lokacin da na zauna gindin wata busasshiyar bishiya sai nan takc ta yi ganye tare da 'yaya Idan na bar gun sai ta koma asalin yadda take."

Yakc cewa "Wata rana ina zaune sai na ji sauti ana ce tnin: Assalamu alaika ya wanda yake daukc da hasken Muhammad (saww) Daga nan sai mahaifinsa Abdul Mutallib ya ce masa: "Ya dana ma maka albishir da Annabin karshen zamani. wanda zai fito daga tsatsonka "

Abdul Mutallib ya taba yin alwashin cewa in Allah (swt) ya ba shi 'ya’ya maza goma zai yanka daya daga ciki saboda Allah Lokacin da "ya yansa.suka kai goma. shida mata. Sai yajdrawo Mazan ya yi musu bayanin alwashinsa. da kumu bukatar yana so ya cika wannan alwashi. sai su duka suka aminta.

Daga nan sai aka yi kuri'a don fitar da wanda za a yanka. Ko da aka yi kuri'a sai kuriata fada kan Abdullahi (as). Duk da tsananin kaunar da Abdul Mutallib yake wa Abdullahi, sai ya kama shi ya nufi wajen da zai yanka domin su kakannin Husain (as) mutanc ne masu gaskiya, nagarta da cika alkawari tun kafui bayyanar Musulunci ga sauran mutanen duniya.

Lokacin da Kuraish. "yan uwan Abdullahi da Mugira Ibn Abdullahi suka ga lallai Abdul Mutallib zai kai ga yanka Abdullahi. sai suka jc don 3u hana shi. sannan suka ba shi shawara a kan ya ban su jo wajen wata  boka a Madina su ba ta labari. ko aaga Karshe za'a. samu mafita wanda ba wannan ba.

Lokaoin da suka isa Madina, suka ba ta labari, sai ta ce musu: Nawa.ne diyyan mutum a wurinku? Sai suka ce rakuma goma 10. Sai ta ce ku je ku yi kuria tsakaninsa da rakuma goma 10, idan kuri'a ta fada kansa, sai ku dinga kara goma-goma har sai Ubangijinku ya yarda. Idan kuri'a ta fada kan rakuman. sai ku kyale shi ku yanka rakuman. Ubangijinku ya yarda kenan a matsayin fansa gare shi.

koda suka iso sai suka bai wa Abdul Mutallib labarin wanna hikimar. Daga sai aka dinga yin kuri'a tsakanin Abdullahi da rakuma. har sai da rakuman suka kai dari kafin Allah ya yarda kuri'a ta fada kan rakuma.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 next