Tarihin Fatima Zahra [a.s]



Wannan suna Fatima ya kasance abin kauna ne sosai ga Ahlul-bait, suna girmama shi suna kuma girmama duk wacce take da wannan sunan. Daya daga cikin aimajiran Imam Sadik an yi mishi haihuwa. sai Imam ya tambaye shi ya sunanta? Sai ya ce Fatima. Sai Imam ya ce amincin Allah ya tabbata ga Fatima. Amma tunda ka sa mata suna Fatima, to kada ka mare ta, kada ka zage ta, kuma ka girmama ta.

Ni kuma nace to wannan ya zama ishara kenan ga "sister" sai a mike tsaye gun tarbiyya don in ba tarbiyya mai kyau to abin da zai biyo baya shi ne abin da Imam Sadik (as) ya ce kada a yi ga mai suna Fatima. Allah ya ba mu dacewa, amin.

5.  Wata rana Imam Ja"afar (as) ya tambayi almajiransa ko sun san TAFSIRIN Fatima? Sai suka ce ba mu sani ba. ya shugabanmu. Sai ya ce an yaye ta ne daga dukkan sharri: Ba ta da sharri ko kadan. Ba don Imam Aliyu ne ya aure ta ba. to da babu wanda zai iya aurenta. mutum ne ko waninsa.

Wadannan Hadisai da muka zo da su ba ruwayar Shi'a ne kawai ba. akwai ruwayoyin sunni masu yawan gaske. wadanda suke bayyana falalar sunaft wannan baiwar Allah. Nana Fatima (as) kamar: a  Sahihul Bukhari

b.  Sahihul Muslim

c.  Sunan Tirmizi

d.  Sunan Nisa'i

e.  Sunan Abi Dauda

f.  Sunan Ibn Maja

Wadanan sune sihahu sitta. Mun zo da misalin su ne a takaice don gudun tsawaitawa. amma mai karatu yana iya bincikawa.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 next