Tarihin Fatima Zahra [a.s]



 

SUNAYEN FATIMA (as)

Aslan sanya suna yana samuwa ne ta hanyoyi biyu: Na farko shi ne ta hanyar "FIDIRA" watau ta hanyar al'ada ta mutum ko mutane, kamar yadda Allah (swt) ya sanar da Annabi Adam sunayen kayayyaki da amfaninsu, inda Allah (swt) yake cewa: "Sai ya sanar da Adam dukkan sunayensu."

Wannan shi ne ta hanyar da muiane suke bi ta wajen sanya sunayen 'yayansiu don wani dalili na addini ko al'ada da sauransu. Amma na biyun kuwa shi ne sanya suna na manyan waliyyan bayin Al-lah, wanda shi Allah (swt) da kanshi ne yake jibintar sanya wannan sunati, kamar sunan Annabi Adam, Hawwa'u (as), Annabi Isa (as) Annabi Yahaya (as). Annabi Muhammad (saw), Nana Fatima (as). Imam Hasan (as), Imam Husain (as). Zainab Alkubra (as) da sauransu.

 

(a) FATIMA (as)

Wannan suna yana da tarin bayani wanda ya gajiyar da duk wani alkalami mai rubutu. Kamar yadda muka yi bayani a baya cewa Allah (swt) da kansa ne ya jibinci sanya wannan sunan bayan haihuwarta. don girmamawa gare ta da kuma bushara ga mabiyanta watati shi’ar mijinta da 'ya yanta Ma'asumai.

Hadisai da dama sun zo dangane da wannan sunan, sun hada day 1. Aii samo daga Imam Bakir (as) cewa lokacin da aka haifi Nana Fatima (as) sai Allah ya yi wahayi ga Mala ika Jibrilu (as) da ya gaya ma Manzo cewa Allah (swt) ya yi mat3 suna Fatima (YAYAYYIYA). Cewa Allah (swt) ya yaye ta daga rashm sani (Tun haihuwar ta babu wani abu yyanda bata sani ba).

2 An samo daga Imam RIDHA da Imam Jawad (as) suna cewa mun ji daga Ma arnun yana ba da labari daga Haruna Rashid, shi kuma ya ji daga Mansur, shi kuma yaji Babansa yana cewa wata rana Abdullahi Ibn Abbas ya tambayi Mir awiyya cewa ko ka san dalilin da ya sa aka ambaci Nana Fatima (as) da suna Fatima17 Sai ya ce a'a. Sai Ibn Abbas ya ce an kira ta ne da Fatima domin an yaye ta da shi’arta daga wuta. Haka na ji Manzon Allah yana fadi.

3. An samo daga Imam RIDHA (as) daga Kakanninsa cewa Manzo ya tambayi Nana Fatima (as) cewa "Ko kin san dalilin da ya sa aka ambace ki da Fatima?" Sai Imam Aliyu (as) ya ce menene dalili ya Manzon Al-lah? Sai Manzo ya ce: "Domin an yaye ta da shi'arta daga unta." Ba su ba wutar jahannama.

4.  An samo daga Abi Hasan Alkazim ya ce: Talauci ba ya shiga gidan da
akwai mai suna Muhammad ko Fatima daga cikin mata.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 next