Tarihin Fatima Zahra [a.s]



Daga nan sai na fito ina mai cike da farin ciki. Sai Manzo ya umurci matansa a kan su saka Nana Fatima (AS) a lalle. su yi mata kwalliya in Allah ya so yau za a kai ta gidaii miji. Daga nan sai suka kama yi mata tattali na kai ta gidan miji. suka shafe ta da turare. wata ta tsefe mata gashi. wata kuma ta yi mata kwalliya. sannan ta sanya rigar da Mala'ika Jibrilu ya kawo mata ta Aljanna.

Bayan nan sai Manzo ya kira diyarsa. Fatima tare da Aliyu mijinta. sai ya kama hannun Imam na dama. sannan ya kama haiinunta na hagu ya dora a kan kirjinsa. sai ya sumbance su a goshinsu. Sannan ya kuma kama hannunta ya dora a kan hannun Imam ya yi masu addu a, yana cewa "Allah ya sanya muku albarka ya Aliyu. Madalla da mata diyar Manzon Allah. madalla da miji kamar Aliyu."

Manzo ya dauko alfadarinsa. wanda ake ce ma Shuhaba u sannan sai ya ce ma Sayyida Shugabar matan duniya ta hau. Bayan ta hau sai ya kira Salmanul Farisi ya ce ya ja alfadarin shi kuma yana koro shi daga baya.

Shin mai karatu ka taba jin rin wannan a tarihin duniya ya taba faruwa ga sauran magabata daga Annabawa. Manzanni. sarakuna. masu mulki ko masu kudi? Wannan fa mai koro alfadarin shi ne shugaban halittn baki daya. kuma wace ce aka dauka a kan alfadarin

ne Amirul muminina, dan uwan Manzo, wasiyysinsa, sannan kuma Sarkin yakinsa. Allah  ta'ala ya bar mu tare da son iyalan gidan Manzo, amin.

Zahabi, Askalani da wasu Malaman sunni sun ruwaito daga Ibn Abbas yana cewa "Sad da ake shiga da Nana Fatima dakinta, Manzo yana gabanta Mala'ika Jibrilu yana gefen hannunta na dama, Mika'ilu yana gefen hannunta na hagu, sannan sauran Mala'iku dubu sabain suna bayanta suna tasbihi, suna tsarkake Allah (SWT) har sai da alfijir ya keto!4

Haka nan jama'a daban-daban suka hadu na Aljanu, mutane da Mala'iku wajen kai garan Nana Fatirna (AS). A lokacin da ake taru za a kai ta matan Manzo sun kasance a gaba suna rera wakoki sauran mata suna amsawa kamar haka: Ummi Salma tana cewa:

1. Ku tafi makwabtana da taimakon Allah.
Ku yi godiya gare shi kowane hali.

2. Ku tuna ni'imomin da Madaukakin Sarki.

Ya yi muku na kwaranyewar bakin ciki da damuwa



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 next