Tarihin Fatima Zahra [a.s]



An ruwaito daga Jabir Ibn Abdullahi Alansari yana cewa: "Wata rana mun yi sallar laasar da Manzo mun zauna kewaye da shi. sai wani tsoho daga cikin muhajirun ya zo sai ya ce "Ya Manzon Allah ina jin yiimya ka ciyar da ni. Ba ni da sutura ka tufatar da ni. ni fakiri ne ka wadatarda ni."

Sai Manzo ya ce masa: "A yanzu babu wani abu tare da ni da zan ba ka. amma wanda ya yi num da aikata alheri kamar wanda ya yi ne. ka je gidan Fatima wacce take son Allah da Manzonsa. Tana fifita Allah a kan abin da take so." Sai ya ce "'Bilal tashi ka raka shi gidan Fatima (AS)."

Lokacin da ya isa kofar gidan. sai ya yi sallama da karfi yana cewa: ''Assalmu alaikum iyalan gidan Manzo. matattarar Mala'iku. wurin saukar wahayi daga Allah Ubangiji talikai. Sai ta ce: 'Wa alaikassalam. wanene?" Sai ya ce wani tsoho ne daga cikin LarabaAya. Daga gurin mahaifinki nake. Ya diyar Muhammad. Yunwa nake ji ki ciyar da ni, ki kuma tufatar da ni. Allah ya ji kanki' A wannan lokacin gabaki daya gidan, kwanansu uku.ba su ci abinci ba. kuma Manzo yajsan halin da suke ciki.

Daga nan sai ta dauki shimfidar da Hasan da Husain suke kwana  ta ba shi. ta ce yaje ya sayar. in Allah ya so zai samu biyan bukata. Sai-ya ce "Ya Fatima abinci nake nema har yaushe zan sayar da wannan sannan in ci abinci?" Sai ta mika haniiunta ta ciro wata sarka a wuyanta waece Fatima binti Hamza ta ba ta. ta ba shi ta ce; "ka je  ka sayar da wannan.'"

sayar in Allah ya so zan samu biyan bukata." Sai Manzo ya fashe da kuka ya ce: "Yaya kuwa ba za ka samu biyan bukata ba alhali Shugabar mata baki daya ta ba ka sarkanta "

Daga nan sai Ammar Ibn Yasir ya rmke ya ce: 'Ya Manzon Allah ka yi min izini in sayi sarkar nan." Sai ya ce "Na maka izirti ka saya Ammar." Da Aljanu da mutane baki daya za su hada kudi su sayi sarkar nan da Allah ba zai musu azaba ba baki daya (wannan yana nuna kaiwa matuka ne wajen darajar abin da yake na Fatima ne a wajen Allah ko da abin wuya ne. bare tufafi. bare "ya'yanta. bare kuma ita kanta)."

Sai Ammar Ibn Yasir ya ce ma tsohon nawa zan biya'.' Sai ya ce "Ba ni abinci da nama wanda zan ci. da bargo sakar Yaman wanda zan dingarufamasallahdashi.dadinarwandazankaiwaiyalina' SaiAmmar ya ce "Na saya a kan dinarc 20 da dirhami dari da bargo sakar Yaman da abin hawa da kuma abinci da nama wanda za ka ci yanzu "

Sai ya bi shi gida ya dauko wannan kudin da kayan ya ba tsohon. Sai tsohon ya koma masallaci da kudin da kayan ya nuna wa Manzo. Ya ce "Yanzu na koshi. na samu sutura kuma talaucina ya kau. Sai Manzo ya ce "To dama za ka saka wa Fatima'.'" Sai ya yi mata addu’a yana cewa: Ya Ubangiji kai ne abin bautar da ya kewaye komai da sani ba sai an ba ka labari ba. kai kadai ne abin bauta a gare mu. kana azurtawa ta duk hamar da ka so. ka bai wa Fatima abin da ido bai taba gani ba. kunne ba taba ji ba

Bayan nan sai Ammar ya dauki sarkar ya fasa masa turare. ya lullube shi da bargo sakar yaman ya bai wa wani bawa nasa mai suna Sahanm ya kai wa Manzo kyauta har shi kansa bawan. Da ya sanar da Manzo da sakon sai Manzo ya tura shi da sakon duk giirm Fatima ko da taji sakon sai ta amsln sarkarda bargon ta kuma "yanta bawan. Ko da bawan ya ji ta yanta shi. sai ya fashe da dariya Sai ta ce 'Mc ya ba ka dariya?"' Sai ya ce yana mamakin albarkar wannausarkan ne. ta ciyar da miskim. ta tufatar da shi. ta wadata shi. ta "yanta bawa. a karshe ta komo hannun mai ita.

An samo daga Abi Sa'idul khudiri yana cewa: "Wata rana Aliyu bn Abi Talib ya wayi gari yana mai matukar jin yunwa. Sai ya tambayi Fatima  akwai abinci? Sai ta ce masa babu komai sai dan abin da Hasan.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 next