Tarihin Fatima Zahra [a.s]



Ya Ummul Hasanaini ya Khaira nisa'il alamina Batula.

An ruwaito daga Imam Sadik yana cewa: Lokacin da Nana Khadija (as) ta auri Manzo matan Makka sun kaurace mata ba sa magana da ita, kuma ba sa bari sauran mata su yi hulda da ita. wai don ta kaskantar da kanta ta auri maraya waoda bai da komai, musamman in Manzo ya fita ba ya tare da ita, Amma lokacin da ta dauki cikin Nana Fatima (as) sai ya zama tana debe mata kewa. ta wajen hira da kuma ba ta hakuri a kan abin da yake samun ta a tafarkin Allah.

Mustapha Limanci cikin wake yana cewa: Yar Manzona a ya Fatima na gaishe ki Tun kan zuwanki ake ganin karama. Allahu shi ya sanya Fatima sunanki. 'Yar Manzona a ya Fatima na gaishe ki. Tun.kina ciki a kwance. kin wa Khadija zancc. Wa ke hakan ga Fati. sai su Fatima Mazajen aiki. 'Yar Manzona a ya Fatima na gaishe ki. Wallahi Fatima gaishe ki. Labbaiki Fatima Labbaiki.

Wata rana Manzo ya shigo gida sai yaji Khadija na zancc. ko da ya tambaye ta. sai ta ba shi labarin cewajaririn da ke cikinta ne yake zancc da ita. Sai Manzo ya ce "Mala'ika Jibrilu ya yi min albishir a kan cewa mace ce mai tsarki. mai yaduwa. kuma Allah (swt) zai sama zurn ata su fito daga gare ta Kuma zai sama shuwagabaiini daga 'ya'yanta. wadanda za su shiryar da al"umma bayan daukeyyar wahayi." Ma'ana bayan wafatin Manzo (saw).

 

Fadalu Ibn Umar ya tambayi Ja'afarus Sadik (as) game da haihuwar Nana Fatima (as) sai ya ce: Lokacin da nakuda ya sauka ma Khadija (as) sai ta aike ma matan Kuraishu da na Banu Hashim a kan su zo. Sai suka aiko mata a kan ba za su zo ba, ai tun farko ta ki jin maganarsu ta auri Muhammad. wanda ba shi da komai, ga irin ta nan ba za su zo ba. Wannan ya sa Nana Khadija (as) ta ji haushi sosai. Nan take sai ga wasu mata guda hudu sun shigo sun yi tsaye gabanta kamar matan Banu Hashim, sai suka yi mata sallama. Daya daga cikinsu ta ce "Kada ki ji tsoro kuma kada ki yi bakin ciki. Mu Manzannin Ubangijinki ne. Ni ce Saratu (matar Annabi Ibrahim). wannan ita ce Asiya bintu Muzahim (matar Fir'auna). Kawarki ce cikin Aljanna, wannan Maryam ce binti Imrana. wannan Safura ce binti Shu'aibu [Matar Annabi Musa (as)]. Allah ne ya aiko mu zuwa gare ki don mu yi miki ungozoma."

Daya ta zauna a gefenta na dama, daya gefenta na hagu, daya a baya. daya kuma a zaune gaba gare ta. Sai Nana Khadija (as) ta haifi Nana Fatima (as) tsarkakakkiya abar tsarkakewa. Yayin da ta fado, haske ya bayyana turt daga dakin har sai da ya haske Makka baki daya. Babu wani guri a bayan kasa wanda wannan hasken bai haske shi ba. Mustapha Limanci cikin wake yana cewa: 'Yar Manzona a ya Fatima na gaishe ki. Ran haihuwarki Zahra haske yai ta kwarara, Mala'ikun Tabara sun zo gurin suna gaishe ki. 'Yar Manzona a ya Fatima na gaishe ki. Labbaiki Fatima Labbaiki.

Ke a cikin mata hudun nan da aka yi wa baiwa ta darajan nan. a cikinsu babu mai kamo ki,

Sai wacce takc gaba gare ta ta dauke ta. Sannan matan Aljanna guda goma suka shigo. kowacce rikc da tasa ta Aljanna cikc da ruwan Alkausar. Sannan wannan wacce ta dauke ta ta amshi ruwan ta yi mata wanka da shi. ta amshi wasu tufafi masti fari. sun fi nonpc ga kamshi wane Almiski. ta lullube ta da shi. Sannan suka nemi NanaTatima (as) da ta yi magana. Daga nan sai Nana Fatima (as) ta fara furuci da cewa: Ta shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah. kuma ta shaida cewa Mahaifinta Manzon Aiiah ne. sannan ktsma mijinta wasHyin Babanta ne.

Nana Khadija (as) ta kasance kamar sauran mataii Larabawa. Takan bayar da 'ya'yanta ne ga shayarwa, amma kan Nana t-atima ai amann sai dai da kanta. Hausawa na cewa "Bigi sai Bigi," ita ce ta jibinci shayar da ita. Kenan a nan muna iya ganin wannan falala da daraja wadda Nana Fatima (as) ta kebantu da shi birbishin sauran 'yan uwanta na haihuwa. Babu wani wanda yake da hannu wajen tarbiyyarta bayan Allah da Manzonsa da kuma uwargidansa Nana Khadija (as).



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 next