Tarihin Fatima Zahra [a.s]



Zaharau Fatima izuwa Allah ita ce Wasila

NANA FATIMA (as) CIKIN KURKUKU DA KUMA TAKUNKUMIN LARABAWA

kamar yadda muka yi bayani can baya cewa an haifi Nana (as) ne bayan wahayi ya sauka da shekara biyar. A wancan Iokacin Manzo bai gushe ba face yana kiran mutane ya zuwa bautar Allah (swt) shi kadai. Maimakon su amsa mishi. sai suka shiga azabtar da shi da mabiyansa, musamman ma wadanda suke da rauni ko kumabayi daga cikinsu, kamar su Bilal (ra) wanda afce daure kafarsa a jikin doki a.sa dokin ya dinga jan shi a cikin garin Makka lungu-lungu. Ko kuma in rana ta yi zafi a fito da shi a tube mashi riga ya kwanta a kan yashi mai tsananin zafi, a sanya masa babban dutse a ciki. wai don ya bar Musulunci. Wannan kuwa bai kara masa komai sai imani. Har shi da kansa yake cewa "Ku ba ni labari idan dayanku yana so ya sai tukunya mai kyau a kasuwa, ai ba zai saya ba har sai ya kuankwasa tukuna kafin ya ba da kudi. to shi ma Allah (swt) haka ne, sai ya kwankwasa tukuna." Kamar Kabbab Ibn Haris. wanda ake sa ya hura wnta irin ta kira. wadda ake sa karfe ya yi ja. sannan a ce ya tube rigarsa ya kwanta da baya har sai yyutar ta mutu.

Sai da ta kai bayansa ya yi bakin kirin kamar man kwalta. har wata rana ya zo gurin Manzo yana kuka a Ka'aba. ya tube rigarsa ya ce Ya Rasulullah dubi bayana yadda ya zama, ka ba mu izini mana mu shata layi." Sai Manzo ya ce mashi ka yi hakuri lokaci yana nan tafe in Allah (swt) ya so. Yacigabadagayamasacewaacanbayaakwai wadanda ake sa zarto ana tsaga su biyu. ko kuma a sa matsefin karfe a wuta har sai ya yi ja sannan a dinga tsefe naman jikinsu har su yi shahada ba su yarda su yi ridda ba.

Kamar su Ammar Ibn Yasir da Babansa da Mahaifiyarsa wanda a karshe aka turkc ta tana da ciki aka daga mashi aka tsira mata a farji take ta yi shahada. Wanda ire-iren wannan suna da yawa. har sai da ta kai Manzo ya yi musu umurni ko kuma izini da su yi hijira zuwa Habasha ko sa samu dan sauki daga wannan mawmacinhalin. Amma shi Manzoyana cikin garin Makka yana ta ci gaba da da'awa a wannan yanayin mai tsanani har sai da Allah (swt) ya cika haskensa. addini ya tabbata. Kamar yadda Malam Ibarahim Zakaky (H) yake cewa, duk abin da azzalumai suke son su yi wa 'yan uwa na kisa ko dauri da sauransu za su iya yi, amma sun yi kadan su hana tabbatar addini a wannan kasar!!!

Lokacin da kafiran Makkah suka ga abin ya ki, kullurn karuwa ake, ana musulunta duk da wadannan matakan da suka dauka, sai suka yanke shawarar su kashe Manzo kawai!! Lokacin da Abu Talib (as) ya ga haka. sai ya tattara Banu Hashim da Banu Mudallib a cikin wani kogo nasa ya yi musu bayani cewa ya zama wajibi a kansu su ba Manzo kariya matukar suna raye. Duk cikansu ba wanda ya ki aminta, sai Abulahabi marashin arzikin duniya da lahira.

Manzo ya kasance da muminai a wannan kogon, wanda ya zama musu kurkuku ba fita ko'ina. Sun kasance cikin tsanani mai yawa na rashin ci da sha, wurin kwanciya ba shimfida bare filo, ba sutura da sauransu. Wannan kuwa ya biyo baya ne saboda yarjejeniyar da aka yi tsakanin Gwamnati da sauran jama'an gari a kan ba za su sayar musu da abinci ba ko abin sha ko wani abin bukata na dan Adam. komai kankantarsa kuma ko nawa za su saya. A wannan lokacin ne idan mutum yaje kusa da kurkukun ba abin da zai ji sai kukan yara kanana da kuma mata. Saboda yunwa da kishirwa har sai da ta kai ga sukan ci ciyawa ne don su rayu. Sun rame kowa kana ganin hakarkarinsa a fili ga kuma rashin lafiya!!! kai har sai da su kansu makiyan nasu. wadanda suke zuwa kallon su suna musu dariya da lzgilanci. suka fara satar jiki a asirce suna kai musu abinci.

To mai karatu kana iya tambaya a nan ka ce yaya labarin Nana Fatima (as) yake a wannan bakin yanayi? Ita dai Nana faj a wannan lokacin tana hannun mahaifiyarta Nana Khadija (as) tana shayar da ita. A lokacin duka shekarunta kusan biyu ne a duniya. Ta bude ido ba ta garnn komai sai takura da tsanani wanda Mahaifinta yake ciki. Ba ta jin komai sai kukan yara da mata kamar yadda muka yi bayani. A cikin wannan yanayin aka yaye ta. Ta fara tafiya. ta koyi magana. Ta kasance cikin wannan halin.har tsawon shekara uku. Sun fito daga wannan kukukun tana da shekara biyar a duniya. Bayan fitowarsu an ce wannan abu ya yi tasiri sosai a wurinta. Ta yadda ta iya fliskantar matsaloli daban-daban don daukaka addinin Allah (swt).

Mai karatu yana iya tunawa cewa wannan sunnar ta gudana ga Malam Ibrahim Zakzaky. da mabiyansa. Bayan an kama shi. aka rusa gidansa aka kasha kauansa aka kuma hana ma  iyalansa wurin zama. Daga karshe aka kama duk iyalansa baki daya har da dan jariri, Harnmad Ibn Ibrahim, wanda bai fi wata shida a duniya ba, aka kulle su a caji ofis (police station). Wanda 'yan uwa sun fito don nuna rashin yarda a Kaduna, Gwamnati ta turo sojoji da 'yan sandan kwantar da tarzoma suka dinga harbi da bindiga har sai da "yan uwa sama da goma zuwa ashirin suka yi shahada, ciki har da Jibrin Mai takarda. Allah muna kokawa zuwa gare ka. ka isar mana kamar yadda ka isar wa Manzonka. Ka kuma ba mu sabati komai tsanani, amin.

A shekara ta uku bayan Manzo da muminai sun shiga wannan yanayin cikin wannan kurkukun, sai Allah (swt) ya yi wa Nana Khadija (as) rasuwa, wanda wannan ya fi girgiza su fiye da halin da suke ciki, musamman ma ; shi Manzo (as) da diyarsa Fatima (as).

A cikin wannan lokacin ne rashin lafiya mai tsanani ya kama Nana Khadija (as) har ta samu shu'urin cewa za ta koma ne ga Ubangijinta Madaukaki Takan kira Nana Fatima (as) ta zaunar da ita kusa da ita tana kallon ta kallo na tausayi da bankwana. tana kuka ita ma Fatima (as) tana kuka. Har sai da Asma'u binti Umais ta ce mata "Ya Khadija me ke sa ki kuka ne, Ashe ba ke ce Shugabar matan Aljanna ba9 Ba ke ce matar Shugaban Ma'aika ba'? Ashe Manzo bai yi miki albishir da Aljanna ba? To me ya sa kike yawaita kuka9" Sai ta budi baki ta ce mata 'Ba wani abu ke sa ni kuka ba. sai dai zan yi wafati in bar Fatima (as) tana karama. wanda nan gaba in ta yi aure ba wacce za ta dinga gaya mata aFamuranta na sirri. Kin san 'ya mace kuwatana bukatar wacce za ta dinga gaya mata sirrinta bayan ta yi aure." Daga nan sai Asma'u binti Umais ta ce mata "Na yi miki alkawari mutukar ma raye zan wakilce ki a wannan lokacin.' Gaskiya ne hakika Asmau ta cancanci yabo. domin ta cika alkawan Duk haihuwar da Fatima (as) take yi Asma'u ne ke yi mata ungozoma. kuma ta yi rmya ta yi tsaki cikin aFamuran Fatima (as) har zuwa wafatinta.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 next