Tarihin Fatima Zahra [a.s]



1. Fatima ma'ana fansar me son ta a rali Kiyama,

Ma"asuma Tsarkakakka ba ta sabo ko alama.

Dahiratun, Mudahhira sunaye nata ne da Umma,

Ga Ummu Abiha khusushya tata ce Rahima.

2. Me dimbin karamomi sunanta ne Karima,

Saboda juriyarta anai mata ma lakabi Halima,

Kubutacciya ga aibi don sunanta ne Salima.

3. Me tsarkin waje da na boye stamfinai Batula.

Ga Mujahida wa ya'kai ta yawan azumi da salla?

Munira kodayaushe tana haske ne kamar fitilla.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 next