Tarihin Fatima Zahra [a.s]



WALIMAR AUREN NANA FATIMA (AS) Manzo ya kirawo Imam Aliyu (AS) yana gaya masa cewa Ya Aliyu aure tare yake da walima' A gurin akwai Sa ad Ibn Mu'az, sai ya ce: Ina da rago. sai ya bai wa Imam. sannan sauran sahabbai suka kawo masa kyautar hatsi da wasunsu. Sannan Manzo ya amshi wancan kudin da ya bai wa Unmii Salma (dirhami goma) ya bai wa Imam ya ce ya je ya sayo dabino da mai da wasunsu. Imam ya je ya sayo ya kawo ma Manzo. Manzo ya jibinci kai-komo wajen hada kayan abincin walimar. Daga nan sai Manzo ya ce ma Imam ya je ya kirawo mutanen da ke masallaci bayan jama'ar da suka taru. Duk jama' sun zazzauna don su sami albarkar da ke clkki wsSta&n walima. Sai Imam ya ce wa Manzo jama'a fa sun taru da yawan gaske. yana ganin abincin ba zai isa ba. Sai Manzo ya ce ba komai a dinga shigo da mutum goma-  goma in sun fita wasu su shiga.

Manzo da kansa yake zuba abincin, Abbas, Hamza, Aliyu da AkilU su ke bai wa tnutane. A haka aka dinga ci, anuna abincin ko raguwa ba ya yi. Sannan Manzo ya ce a kawo'babban kwano ya deba ma fakiran Madina, wadanda ba'sa rian. Sannan ya ce "Wannan ragowar kuwa na Fatima ne da mijinta." AHahu akbar, wannan shi ne walima mafi daraja da aka tabayi a doron kasa.7 KAI GARAN NANA FATIMA

An ruwaito Imam Aliyu (AS) yana cewa "Na zauna bayan aure na wasu 'yan watanni ban taba yi wa Manzo magana ba kan danga ne da al amari na Fatima saboda kunya, sai dai duk lokacin da muka kebanta da Manzoyakan ce min 'Ya Aliyu me ya yi kyawun hali, halitta da dibi'a irin matarka? Ina yi maka albishir da ce-wa na aurar maka da shugabar matan duniya ne baki daya.'

Imam ya ci gaba da cewa: "Bayan wannan lokutan sai dan’uwanka Akilu ya zo gurina yana cewa: 'Ba abin da ya taba faranta min rai kamar aurenka da Fatima, 'yar Muhammad (SAW). Ya dan’uwanka me zai sa ba za ka yi wa Manzo maganar tarewa ba. ko ka kasance tare da abar kaunarka'.r Sai na ce wallahi wannan shi ne mafi soyuwa a gare ni. amma ba abin da ke hana ni sai kunya.

"Daga nan sai ya ce mu je gun Manzo tare. Mun fito muna tafiya sai muka hadu da Ummu Aiman. Sai muka ba ta labarin abm da yake akwai. Sai ta ce mu koma mu bar alamarin a hannunsu. Wannan al amarin na mata ne. sai su

"Daga nan sai ta nufi gidan Ummi Salma ta ba ta labari tare da sauran matan Manzo baki daya. Matan Manzo gaba daya suka hadu ga Manzo a tare da su. Sai suka ce ' Uwayenmu da Ubanninmu fansarka ne ya Manzon Allah. Babban alaman ne ya hada mu a nan. wanda da Khadija na da rai da ya faranta mata rai'

"Sai Ummi Salma ta ce: Lokacin da muka ambaci sunan khadija sai hawaye suka zubo masa daga ldo. Sai ya ce 'Khadija. wacecc za ta yi kama da Khadija? Ta gaskkata ni lokacin da mutanc suka karyata ni, ta taimake ni a cikin addinin Allah. ta kuma taimaka min da dukiyarta. Allah Mabuwayi da daukaka ya umurce ni da in mata albishir da gida a cikin Aljanna. babu wahala ko bakin ciki a cikinsa'

Sai muka ce 'Ya Manzon Allah. ba wani abu da za ka fadi game da Khadija face haka yake, duk da dai ta koma ga Ubangijinta. Muna fatan Allah ya hada mu da ita cikin Aljanna Madaukakiya da rahamarsa. Ya Manzon Allah, dan uwanka ne na addini kuma dan Amminka ta nasaba, Aliyu Ibn Abi Talib yake so amaryarsa, Fatima tatare."

Sai Manzo ya ce: 'Ya Ummi Salma me ya sa tun tuni Aliyu bai min magana ba?' Sai ta ce kunya ce take hana shi. Sai Manzo ya ce wa Ummu Aiman ta je ta kira Aliyu. Ko da ta fito sai ta ga Aliyu ya zauna yana sauraron labarin yadda aka kaya. Sai ya ce mata 'yaya labari?' Sai ta ce Manzo yana kira."

Imam ya ce: "Da na shiga sai matan Manzo suka mike suka shiga cikin dakuna. Sai na zauna gabansa, kaina yana kallon kasa don kunya. Sai ya ce min kana so matarka ta tare? Sai na ce na'am. Sai ya ce "Madalla. yau ko gobe in Allah ya so za ta tare."



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 next