Tarihin Fatima Zahra [a.s]



Ya zo a ruwayar sunni daga SAFURI ASSHAFFI cewa lokacin da Allah (swt) ya halicci Annabi Adam (as) har zuwa inda ya ce sai Annabi Adam (as) ya ga wata Budurwa kyakkyawa tana haske. haske mai wulkawa ga kambun Azurfa a kanta ga lu'ulu'u kewaye da ita. Annabi Adam (as) bai taba ganin kyakkyawar mace irinta ba. Sai ya ce ya Ubangijina wacece waccan? Sai aka ce mishi Fatima ce Sar Muhammad Manzon Allah Sai ya ce wanene zai zama mijinta?

Sai Allah (swt) ya ce ya Jibrilu bude waccan dakin na yakutu. Ko da aka bude masa sai ya ga wani saurayi zaune a kan gadon zinare kyawunsa kainar na Annabi Yusuf (as). Sai aka ce mishi wannan shi ne mijinta Aliyu Ibn Abi Talib.

Wannan kadan kenan. Mun yi haka ne don gudun kada littafin ya yi tsawo don na yara ne 'yan Fodiyya. Amma mai karatu yana iya fadada bincike. Allah ya yi mana muwafaka. amin.

 

(b) SIDDIKA (as)

Siddika: Ma'ana: Mai yawan gaskiya, wadda ba ta taba yin karya ba a rayuwarta, mai kamala ta gaskiya. wadda ba ta taba murguda gaskiya ba. wadda ayyukanta suke gaskata zancenta. wadda ta bayyanar da gaskiyarta a aikace. Allah yana cewa: "Almasihu dan Maryam bai kasance ba sai dai Manzo ne, Manzanni kuwa sun wuce kafinsa, kuma mahaifiyarsa maiyawan gaskiya ne."

Allah (swt) ya ambaci Maryani (as) a naii da mai yawan gaskiya ce don saboda gaskatawarta ga ayoyin Ubangijmta. matsayin danta da abin da ya ba da labari a kai. Ba a taba jin karya dadai a bakinta ba.

Saudayawa mutum yakan saba ma Allah alhali yana mai gaskatawar Allah yana ganin sa. Yakan sha giya. ya yi zina. ya ci riba. ba don bai san haram bane ko kuma yyxita ko Aljanna ko sakamakon kiyama gaskiya bane. A'a sai dai ayyukansa ne ba su yi daidai da abin da ya gaskata ba, ko kuma kimar gaskata-warsa ba za ta iya raba shi da wannan mummunan aikin ba.

Daga bayanan da muka yi tnai karatu yana iya ganin cewa lallai "yar Manzo irin Fatima (as) ta tattaro wadannan siffofin, ta taka kololuwar darajar nan na siddikancj. Manzo mai tsira ya kira ta da sunan Siddika. sannan sauran mutane da Aljanu da kuma Malaikun Allah (swt).

An samo daga Manzo yana fadi ma Imam Aliyu (as) cewa: An ba ka abubuwa uku wadanda ba a bai wa kowa ba, har ni:



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 next