Ahlul Baiti



Mafi yawan malaman Imamiyya sun ce baliga shiryayya tana da mallakar dukkan lamurran da suka shafi kulla wata yarjejeniya har da na aure, budurwa take ko bazawara, hakan kuwa saboda balaga da kuma shiryuwarta ne. Tana iya daura aure wa kanta ko waninta, ko ta yi da kanta ko da wakili, ko ta bayar ko karba. Ita kamar namiji take ba tare da wani bambanci ba .

Batun sakin aure kuwa, Abu Zuhra ya fada cikin littafinsa Ahwalul Shaksiyya shafi na 283 cewa: "A mazhabar Hanafiyya saki yana aukuwa ne daga kowani mutum idan ba yaro ko mahaukaci ko mai raunin hankali ba, saboda haka saki yana aukuwa daga mai wasa ko mai maye daga abin da yake haram, ko wanda aka tilasta". A shafi na 286 ya ce: "Tabbatacce yake a mazhabar Hanafiyya cewa sakin wanda ya yi kuskure ko mantuwa yana aukuwa"([248]).

A shafi na 284 kuma ya ce: "Malik da Shafi'i sun dace da Abu Hanifa da mutanensa kan batun sakin mai wasa, Ahmad ya saba da shi, yana ganin rashin aukuwar sakin".

Imamiyya sun ruwaito daga Ahlulbaiti (a.s) cewa:

"Babu saki sai ga wanda ya nufi sakin".

Dangane da iddar macen da ta yi zina kuwa: Hanafawa da Shafi'awa da mafiya yawa daga Imamiyya sun ce: Idda ba ta wajaba domin zina, domin ruwan (maniyyin) mazinaci ba shi da wata alhurma (girmama-wa). Saboda haka ya halalta a daura aure wa macen da ta yi zina, da kuma ingancin takar ta ko da tana da ciki. Amma Hanafawa sun haramta takar mai ciki sai ta haihu duk da yake ana iya daura mata aure.

Malikawa kuwa sun ce: Wanda ya yi zina da mace tamkar takan ta ne cikin rashin sani, dole ne ta yi istibra'i gwargwadon idda sai fa idan ana nufin tsayar da haddi kanta ne, a nan kam sai ta yi istibra'i da haila guda.

Hanbalawa kuwa suka ce: Idda wajiba ce kan mazinaciya kamar yadda take kan sakakka (AlMugni, juzu'i na 6 da kuma Majma'ul Anhar)

Kan batun wasiyya ga ciki (wato dan da ke cikin ciki) kuwa, malaman fikihu sun saba kan cewa shin dole ne a samu cikin yayin wasiyyar ko kuma a'a.

Imamiyya da Hanafiyya da Hambaliyya da Shafi'iyya bisa mafi ingancin zantuttukansu sun ce ana shardanta hakan, kuma cikin ba ya gado sai idan an san cewa samamme ne yayin wasiyyar. Ana tabbatar da hakan ne, idan matar ta haihu kafin wata shida bayan an yi wasiyyar idan tana da miji mai iya saduwa da ita. Idan kuwa ta haihu bayan wata shida ko fiye, to ba a bai wa ciki kome daga cikin wasiyyar saboda yiyuwar samuwar sabon ciki. Tushe shi ne rashin samuwar ciki yayin da aka yi wasiyyar. Wannan kauli kuwa ya ginu ne kan rashin halalcin wasiyya wa wanda ba samamme ba.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 next