Ahlul Baiti



"Ka ba ni labari yaushe ne Allah Ya kasance?, sai ya ce: "Yaushe ne bai kasance ba har zan ba ka labarin lokacin da Ya kasance? Tsarki ya tabbata wa Wanda bai gushe kuma ba zai gushe ba, Makadaici, Wanda ake nufinSa da bukata, bai riki abokiyar zama ba ko kuma da([169])".

Imam Sadik (a.s.) ya ruwaito cewa wani malamin yahudawa ya taho ma Imam Ali (a.s.) yana tambayarsa cewa:

"Ya Amirul Muminina! Yaushe Ubangijinka Ya kasance? Sai ya ce masa:"Tir da kai, ana 'yaushe ya kasance' ga Wanda ba samamme ba ne? Amma wanda samamme ne ba da wani ba, ba a ce wa 'yaushe ya samu'. Shi Allah samamme ne gaban gabani ba tare da wani 'gabani' ba kuma samamme ne bayan 'baya' ba tare da wani 'baya' ba, kuma babu wai iyakar karshe da za a ce karshenSa ya kai iyaka". Sai malamin ya ce da Imam: "Kai Annabi ne?", Sai Imam (a.s.) ya amsa da cewa: "Kaitonka, ni ba kowa ba ne face bawa cikin bayin Manzon Allah (s.a.w.a.) ([170])".

Imam Bakir (a.s.) ya ce:

"Na hane ku yin tunani kan Allah, sai dai duk yayin da kuke nufin duban buwayar Allah to ku dubi girman halittun Allah([171])".

Imam Sadik (a.s.) ya yi wasiyya ga wani sahabbinsa (Muhammad bn Muslim) da cewa:

"Ya Muhammad! Su mutane, magana ba za ta gushe gare su ba har sai sun yi magana kan (zatin) Allah. To idan kun ji ana hakan ku ce: 'Babu abin bauta face Allah Makadaici, Wanda babu wani abu tamkarsa([172])'".

Imam Bakir (a.s.) yana cewa:

"Ku yi magana kan kome, kada ku yi magana kan batun zatin Allah([173])".

Yayin da wani ya tambayi Imam Ali (a.s.) cewa: 'Ina Allah Yake gabannin Ya halicci halitta', sai Imam ya yi masa bayani cewa Allah ba Shi da bukatar bigire, Ya karfafa tsarkakar Mahalicci Madaukaki ga barin wannan, haka nan tsarkakke Ya ke ga barin bukatuwa ya zuwa ga zamani.
Wani mai tambayan kuma ya tambaye shi cewa: 'Ina Ubangijinmu Yake kafin Ya halicci sama da kasa?, Sai Imam (a.s.) ya amsa da cewa: "Ina tambaya ce kan bijire, Allah kuwa Samamme ne yayin da ba a samar da bigire ba([174])".



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 next