Ahlul Baiti



"Dukkan hadisanmu idan ba 'yan kadan ba suna komawa ga Imamanmu goma sha biyu (a.s.), daga nan kuma suna komawa zuwa ga Annabi (s.a.w.a). Domin ilminsu abin haskaka ne daga waccar fitilar([133])".

Da wannan ne Imaman Ahlulbaiti (a.s) suka zama mabubbugar hadisi da ruwaya da bayanin hukumce-hukumcen shari'a da kuma bude boyayyun al'amurranta.

Lalle rayuwarsu mai albarka, rayuwa ce da ke danfare da juna, babu rabewa a cikinta, babu wani bako wanda ba sananne ba da ya shamakance saduwarsu da Manzon Allah (s.a.w.a.), to wannan rayuwa tana zaman wata makaranta ce da kuma gwaji rayayye mai nuna Musulunci da tabbatar da hukumce-hukumcensa da kiyaye tushensa. Dukkan wannan yana karfafa mana amincewa da tsarkin mabubbugar da tsabtar baiwar da kuma cewa abin da ya taho daga gare su (a.s.) mai asali ne.

Yayin da muka san dukkan hakan, za mu iya gane yanayin da mazhabar ilmi wanda mabiyan Ahlulbaiti (a.s) suka taso daga ciki suka kuma dauki iliminsu, sannan za mu gane cewa mazhabarsu na hadisi da tafsiri da ilmin akida da tauhidi da dai sauransu suna da aminci kuma hanya ce tsabtacciya mai sadarwa zuwa ga masaniyar annabci da tsarkin shari'a da asalin tushen Musulunci.

Daga nan ya dace mu fito da daidaikun silsilar nan mai albarka ta Imaman Ahlulbaiti (a.s) maruwaita daga Manzon Allah (s.a.w.a.) sannan kuma mu sanar da al'ummarmu matsayinsu na ilmi a shariance. Su Ahlulbaiti (a.s) yayin da suke zancen silsilarsu ta maruwaita hadisin Manzon Allah (s.a.w.a.), suna zancen wannan silsilar ne, ga ta nan kuwa:

1.  Aliyu bn Abi Talib (a.s.), an haife shi shekara ta 30 bayan Shekarar Giwaye, ya kuma yi shahada ne a shekara ta 40 bayan hijira.

2.  Hasan bn Ali (a.s.), an haife shi shekara ta 3 bayan hijira, ya yi shahada kuma a shekara ta 50 bayan hijira.

3.  Husaini bn Ali (a.s.), an haife shi a shekara ta 4 bayan hijira, ya yi kuma shahada ne a shekara ta 61 bayan hijira.

4.  Imam Ali bn Husain (Zainul Abidin) (a.s.), an haife shi a shekara ta 38 bayan hijira, ya yi shahada a shekara ta 95 bayan hijira.

5.  Imam Muhammad bn Ali al-Bakir (a.s.), an haife shi a shekara ta 57 bayan hijira, ya yi shahada a shekara ta 114 bayan hijira.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 next