Ahlul Baiti



Al-Wakidi ya ce: "Ya kasance mai gaskiya, yana ba da fatawa a masallacin Manzon Allah (s.a.w.a.) alhali yana dan shekara ashirin da 'yan kai. Yana daga dabaka ta takwas ta tabi'ai na mutanen Madina([151])".

Amma babansa Musa bn Ja'afar (a.s.) wanda muka riga da muka san matsayinsa na ilmi da tsantsaini da tsoron Allah, shi ma ya ba da shaidar ilmin Aliyu bn Musa al-Ridha da kuma shiryarwa zuwa ga karbar addini da shiriya daga gare shi, inda yake cewa:

"Wannan dan'uwannaku Ali bn Musa, shi ne mafi sani a duk mutanen gidan Muhammadu, don haka ku tambaye shi batun addininku, kuma ku kiyaye abin da yake fada muku([152])".

9- Imam Muhammad bn Aliyu al-Jawad (a.s.):

Amma Imam Jawad (a.s.), shi ma tamkar mahaifa da magabatansa tsarkaka yake wajen ilmi da zuhudu da kuma tsoron Allah.

Sibd bn Al-Jawzi yana cewa:

"Muhammad al-Jawad shi ne Muhammad bn Ali bn Musa bn Ja'afar bn Muhammad bn Ali bn Husain bn Ali bn Abi Dalib. Sunan kunyarsa shi ne Abu Abdullah, wasu kuma su kan ce masa Abu Ja'afar. An haife shi ne a shekara ta 165 bayan hijira, ya yi shahada kuma a shekara ta 220, ya kasance bisa tafarkin babansa wajen ilmi da takawa da zuhudu da kyauta([153])".

Muhammad bn Ammar ya ruwaito cewa:

"Na kasance wajen Ali bn Ja'afar(*) bn Muhammad a Madina, na kasance a wajensa har na tsawon shekara biyu ina rubuta abin da na ji daga wajen dan'uwansa (Imam Musa bn Ja'afar Kazim) sai Abu Ja'afar Muhammad bn Ali Ridha ya shiga masallacin Manzon Allah (s.a.w.a.), sai Ali bn Ja'afar ya yunkura ya mike ba takalmi ba abaya, sai ya sumbanci hannunsa ya girmama shi.

Sai Abu Ja'afar ya ce da shi: "Ya baffana, zauna mana, Allah Ya yi maka rahama".



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 next