Ahlul Baiti



An samu daga Abu Abdullah, Imam Sadik (a.s.) daga Mahaifansa, daga Imam Ali (a.s.) cewa:

"Kowace gaskiya tana tare da wata hakika, kuma kowace dacewa tana tare da wani haske. To abin da ya dace da Littafin Allah ku karbe shi, abin da kuwa ya saba da Sunnar Manzon Allah, to ku bar shi([127])".

Sannan kuma yana cewa:

"Allah Ya ji kan mutumin da ya kawo hadisi daga Manzon Allah (s.a.w.a.) ba tare da ya yi masa karya ba, ko da kuwa mutane sun guje shi([128])".

Sannan Amirul Muminina Ali (a.s) ya ce: "Na ji Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa:

"Idan hadisi ya taho muku (sashinsa) yana daidaita, (sashi kuma) yana sassabawa, to abin da sashinsa yake karyata sashe ba daga gare ni yake ba, kuma ban fade shi ba, ko da an ce na fada. Idan kuma hadisi ya taho muku, sashensa yana gaskata sashe, to shi daga gare ni yake, kuma ni na fade shi. Wamda kuwa ya ganni bayan rasuwata, kamar wanda ya ganni a raye ne, wanda kuwa ya ziyarce ni to zan kasance masa mai shaida a ranar kiyama([129])".

An samu daga gare shi (a.s.) ya ce wa Muhammad bn Muslim cewa:

"Ya Muhammad! Abin da ya taho maka na wata ruwaya daga mutumin kwarai ko na banza, idan ya dace da Alkur'ani to ka dauke shi, abin da kuwa ya taho maka na ruwaya daga mutumin kwarai ko na banza, idan ya saba da Alkur'ani to kada ka karbe shi([130])".

Haka nan ake sanya iyakoki wa abin da ake daukarsa Sunnar Manzon Allah (s.a.w.a.) ne a mazhabar Ahlulbaiti (a.s) da tafarkinsu da kuma alakar wannan Sunna mai tsarki da Littafin Allah, da kuma rawar da take takawa cikin shari'a da sanya dokoki da gina rayuwar zamantakewa da ta ibada, wa al'ummar Musulmi.

Muna iya tsamo wadansu abubuwa daga wannan tsarin mazhabi kamar haka:



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 next