Ahlul Baiti



Imam Sadik (a.s.) yana cewa:

"Lalle Alkur'ani rayayye ne ba matacce ba, kuma yana gudana kamar yadda dare da yini suke gudana, kuma kamar yadda rana da wata suke tafiya. Yana kuma tafe ne kan na karshenmu, kamar yadda yake tafe a kan na farkonmu".

Amirul Muminina (a.s) ya ce:

"Sannan Allah Ya saukar masa da Littafi, haske ne fitilunsa, ba su mutuwa, fitila ce da haskenta ba ya bishewa, kogi ne da ba a risko zurfinsa; tafarki ne wanda salonsa ba ya bacewa; haske ne wanda ba ya yin duhu, mai rarrabewa wanda karfin hujjarsa ba ya raguwa, bayani ne wanda ba a rusa ginshikinsa, waraka ce wadda ba a tsoron cuta a tare da ita, daukaka ce wacce ba a rinjayar masu taimakon ta; gaskiya ce wadda ba a tabar da masu taya ta. Shi ne taskar imani, kuma tsakiyar shi, shi ne mabubbugan ilmi da kogunan shi; shi ne koraman adalci da tabkunan shi; shi ne murhun Musulunci da ginin shi; shi ne kwazazzabon gaskiya da mafakarta; shi tekun ne da masu kwarfa ba sa iya kwarfe shi; idanuwar ruwa ne masu kwarfa ba su iya karar da shi; wuraren sha ne masu taho masa ba sa kafar da shi; masaukai ne da matafiya ba sa bacewa da hanyarsa, alamu ne wadanda matafiya ba sa makance masa; tsaunuka ne da wanda ya nufe su ba zai wuce su ba. Allah Ya sanya shi mai kashe kishin ruwan malamai; bazaar (mai rayawa) ga zukatan fukaha'u (masana ilmin fikihu); gwadabe mai tara hanyoyin mutanen kwarai; waraka wadda babu wata cuta bayanta; hasken da babu wani duhu tare da shi; igiya ce mai karfi; mafaka ce wadda kololuwarta karerriya ce; daukaka ga wanda ya jibince shi; aminci ga wanda ya shige shi; shiriya ga wanda ya yi koyi da shi; uzuri ga wanda ya yi riko da shi; hujja ga wanda ya yi magana da shi; shaida ga wanda ya yi amfani da shi wajen jayayya; nasara ga wanda ya kafa hujja da shi; mai daukar duk wanda dauke shi; abin hawa ga wanda ya yi aiki da shi; alama (aya) ce ga wanda ya sa lura; garkuwa ga wanda ya nemi kariya da shi; ilmi ga mai kiyayewa; abin fadi ga mai ruwaya; kuma hukumci ne ga mai hukumtawa([105])".

Haka nan dai muke fahimtar kimar Alkur'ani da darajarsa a mazhabar Ahlulbaiti (a.s) da kuma tafarkinsu. Ita ce kuwa kima ta hakika wacce Alkur'ani ya yi furuci da ita, wahayi kuma ya siffanta shi da ita

"Hakika wannan Alkur'ani yana shiryarwa zuwa hanya da tafi daidai". (Surar Isra'i, 17: 9)

Alkur'ani shi ne hanyar rayuwar al'umma, mabubbu-gar ilmi da shiriya, taskar ma'arifa da wayewa, tafarkin fahimta da tunani, ma'aunin ci gaba da halaye na kwarai, shi ne doka ta ilmi wajen tsara rayuwar dan'Adamtaka, kuma shi ne ma'aji mai tattara al'adun rayuwar mutumtaka da dokokinta.

Ka'idojin Fahimtar Alkur'ani Da Tafsirinsa

A cikin abin da ya gabata, mun ambaci yadda tafar-kin Ahlulbaiti (a.s) da mazhabarsu suka tabbatar mana da cewa Littafin Allah madawwami ne, ba jirkitarwar da ta same shi, shi ne kuma kundin dokokin Ubangiji dawwa-mammu, shi ne tushen shari'a, shi ne ma'auni mai hukumci kan ingancin ruwayoyi da hadisai, shi ne kuma hujja wajen tabbatar da kuskure ko dacewar kowane abu. Hadisi ya zo daga Manzon Allah (s.a.w.a.) cewa:

"Idan wani hadisi ya zo muku daga gare ni, ku gwada shi da Littafin Allah, abin da ya dace da shi ku karba, abin da ya saba masa kuwa ku yi jifa da shi([106])".



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 next