Ahlul Baiti



"Ku tsoraci zalunci domin shi duhu ne a ranar lahira([214])".

Imam Sadik (a.s.) ya ce:

"Allah Mai Girma da Daukaka Ya yi wasicci ga wani Annabi da cikin Annabawansa wanda yake cikin masarautar wani jabbarin sarki cewa: 'Ka je wajen wannan azzalumin ka ce da shi; Ni ban shugabantar da kai domin zubar da jini da tara dukiya ba, sai dai kawai na shugabantar da kai ne domin ka raba Ni da sautin (karar) wadanda aka zalunta. Domin Ni ba zan bar zaluncin da aka yi masu ba ko da kafirai ne([215])".

Imam Sadik (a.s.) ya ce:

"Da wanda ya aikata zalunci da mai taimakonsa da kuma wanda ya yarda da shi, to dukkansu ukun masu tarayya ne (cikin zaluncin) ([216])".

Imam Sadik (a.s.) din dai ya ce:

"Duk wanda ya yi uzuri wa zaluncin azzalumi, Allah zai dora masa wani azzalumi da zai zalunce shi, kuma idan ya yi addu'a ba za a amsa masa ba, kuma Allah ba zai ba shi ladar zaluncin da aka masa ba ([217])".

Abu Basir ya ruwaito cewa: "Mutane biyu sun zo wajen Imam Sadik (a.s.) a kan wani lamari na mu'amala tsakaninsu. Yayin da Imam (a.s.) ya ji zancen kowannensu, sai ya ce: "Hakika wanda ya cimma bukatarsa da zalunci bai cimma kome ba. Lallai za a biya wanda aka zalunta da addinin azzalumin fiye da abin da shi ya dauka daga dukiyar wanda aka zalunta", daga nan sai ya ce: "Duk wanda yake aikata wa mutane sharri kada ya yi kyama idan aka yi masa. Hakika babu abin da dan Adam zai girba face abin da ya shuka. Babu wanda zai girbi abu mai dadi baicin ya shuka mai daci, babu kuma wanda zai girbi mai daci baicin ya shuka mai dadi". Sai mutane biyun nan suka yi sulhu kafin ma su tashi daga gare shi ([218])".

A'imman Ahlulbaiti (a.s) sun ruwaito cewa Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce:

"Duk wanda ya tafi tare da azzalumi domin ya taimake shi, alhalin ya san cewa shi azzalumi ne, to, hakika ya fice daga Musulunci ([219])".



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 next