Ahlul Baiti



Har ila yau an sassaba a kan ma'anar aalu, wasu sun ce su ne danginsa, wasu kuma sun ce su ne al'ummarsa. To idan mun dauke shi da ma'anar dangi, to su din dai su ne aalu din, idan kuma muka dauke shi da ma'anar al'umma([10])wadanda suka karbi kiransa to nan ma dai su ne aalu din. Don haka a bisa dukkan yanayi dai su aalu din ne dai.

To amma shigar waninsu cikin kalmar aal, a nan kan an samu sabani kan hakan. Marubucin al-Kashshaf ya ruwaito cewa yayin da wannan aya ta sauka, mutane sun ce: "Ya Manzon Allah su waye danginka wadanda kaunarsu ta wajaba a kanmu? Sai ya ce: "Aliyu, Fadima da 'ya'yansu biyu", sai ya tabbatar da cewa wadannan hudun su ne dangin Annabi (s.a.w.a), to idan kuwa hakan ya tabbata to ya wajaba su zama abin kebancewa da karin girmamawa. Ana iya tabbatar da hakan ta fuskoki kamar haka:

1.  Fadin Allah (S.W.T) cewa: "face dai soyayya ga makusanta", kuma fuskar kafa hujja da ayar ya gabata.

2.  Babu shakka cewa Annabi (s.a.w.a) ya kasance yana kaunar Fadima. An ruwaito shi yana cewa:

"Fadima yanki ne daga gare ni, abin da yake cutar da ita yana cutar da ni ".

Kamar yadda ingantaccen hadisi ya tabbatar cewa Annabi Muhammadu (s.a.w.a) ya kasance yana kaunar Aliyu, Hasan da Husaini (a.s.). To idan wannan ya tabbata, lallai kaunarsu ta zama wajibi a kan dukkan al'umma domin fadin Allah (S.W.T.) cewa:

"Ka ce: Idan kun kasance kuna son Allah, to ku bi ni, Allah Ya so ku...". (Surar Ali Imrana, 3:31)

"...ku bi shi, don ku shiryu". (Surar A'arafi, 7: 158)

Da kuma fadinSa cewa:

"...to, wadanda suke sabawa umurninSa, su kiyayi abkuwar wata fitina...". (Surar Nur, 24: 63)



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 next