Ahlul Baiti



1.    Cewa kowane fadi ko aiki ko tabbatarwar da aka danganta ga Manzon Allah (s.a.w.a.), to wajibi ne a gwada su da Alkur'ani, a tabbatar da ingancinsu bisa hasken Alkur'ani, abin da ya dace da Littafin Allah, to daga Sunnar Manzo (s.a.w.a) yake, abin da kuwa ya saba da shi to ba kome yake ba wajen Sunna.

2.  Alkur'ani da Sunna su ne tushen shari'a da doka, su ne ma'aunin hukumce-hukumce da halaye da tsarin rayuwa. Abin da duk muka samu na hukumce-hukumce na fikihu ko ma'anonin da ake riska na akida, to wajibi ne mu tabbata sun dace da Littafin Allah da Sunna. Duk abin da muka samu daga cikinsu ya dogara bisa asasin Littafin Allah da Sunna da shari'a, to doka ce ta Allah, mu yi aiki da shi, mu rike shi da karfi. Abin da kuwa ya saba da Littafin Allah da Sunna to shi bidi'a ce, bata ce.

3.  Idan aka samu Sunna tabbatacciya, wacce an tabbatar da fitowarta daga Manzon Allah (s.a.w.a.) tana kuwa yin daidai da Litttafin Allah, to wajibi ne mu dauke ta a matsayin ma'auni kuma abin da za a yi amfani da ita wajen ruwayoyi da hadisan da muke shakkar su, ko muka sami rikitarwa wajen ingancinsu. Sai mu tabbatar da abin da ya dace da Littafin Allah da tabbatacciyar Sunna, mu yarfar da abin da ya saba da su. Ta wannan hanyar ne mazhabar Ahlulbaiti (a.s) ta ke iyakance tafarkin da za a bi wajen mu'amala da Sunnar Ma'aiki (s.a.w.a.).

Rabe-Raben Sunnar Annabi (s.a.w.a):

Malamai suna raba Sunnar Annabi (s.a.w.a) zuwa gida uku:

1.  Maganganu: Su ne dukkan abin da suka taho daga Manzon Allah (s.a.w.a.) na daga zantattuka, hudubobi, wasiyyoyi, wasiku da dai sauransu.

2.  Ayyuka: Abin nufi shi ne duk wani aiki da Manzon Allah (s.a.w.a.) ya yi wajen mu'amalarsa da mutane, ko wajen yin ibadoji, ko wanin wannan daga abin da yake bayyana halalci. Duk aikin da Manzon Allah (s.a.w.a.) ya aikata to za mu gane halalcinsa a tushen al'amarin domin Ma'aiki (s.a.w.a.) abin tsarakake-wa ne daga aikata haramun.

Saboda haka muna iya cewa abin da ya fito daga Ma'aiki (s.a.w.a.) na aiki ya kasu kashi biyu:

·  Wajibci: Sashin abin da ya fito daga Manzo (s.a.w.a) kamar salla, hajji, adalci tsakanin mutane da dai sauransu, yana bayyana wajibcin wannan aiki, da kuma cewa shi takalifi ne kuma farilla ne, wadda lizimtar su yana wajaba a kanmu, kuma dole ne mu gudanar da hukumce-hukumcensu.

·  Akwai wasu ayyukan Manzon Allah (s.a.w.a.) wadanda ba su nuna wajibci, suna nuna halalci ne. Dukkan wannan yana karkashin halal, wanda aikatasu ja'izi (ya halalta) ne.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 next