Ahlul Baiti



"Idan kun ki yarda da mubahala, to ku musulunta duk hakkin da musulmai ke da shi kuma kuna da shi, duk kuwa abin da yake kansu yana kanku". Amma sai suka ki, don haka sai ya ce musu: "To ni zan yake ku".

Sai suka ce : "Ba mu da karfin yaki da Larabawa, amma za mu yi sulhu da kai cewa ba za ka kai mana hari ba, ba za ka tsoratamu ba, ba za ka fitar da mu daga addininmu ba. Mu kuma za mu kawo riguna dubu biyu duk shekara, dubu daya cikin watan Safar dubu dayan kuwa cikin watan Rajab, da kuma sulken karfe guda talatin". Sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya yi sulhu da su akan hakan, sa'an nan ya ce:

"Na rantse da Wanda raina yake HannunSa, hakika

halaka ta yi reto kan mutanen Najran, da sun yi mubahala (da mu) da anshafe su an mai da su birrai da aladu, da kuma kwazazzabon nan ya kama da wuta a kansu da kuma Allah Ya tuge Najran da mutanenta har tsuntsayen da ke bisa bishiyoyi, kuma da ba za a shekara ba face Nasara sun hallaka dukkansu".

Sannan Zamakhshari ya ci gaba da bayani kan tafsirin Ayar Mubahala da matsayin Ahlulbaiti (a.s) bayan da ya ba da shaidar matsayinsu mai girma da hadisin Ummul Muminina A'isha, ya ce:

"(Annabi) Ya gabatar da su (Ahlulbaiti) a kan kansa ne wajen ambato domin ya yi mana tambihi a kan taushin matsayinsu da kusancinsu (ga Allah), don ya nuna cewa su abin gabatarwa ne a kan kai kuma abin fansa da su. Wannan kuwa shi ne mafi karfin dalili a kan falalar Ashabul Kisa'i([17]).

Tafsirul Kashshaf na Zamakhshari yayin tafsirin Surar Ali Imrana aya ta 61, haka nan kuma ya zo cikin Tafsirin Tha'alabi daga Mujahid da Kalbi([18]).

Wannan yanayi (na fitowa domin Mubahala) yana nuna mana fitowar rundunar imani ne tana fuskantar rundunar shirka, sannan kuma wadanda suka fito (a sashin imani) su ne 'yan kan gaba wajen karbar shiriya, su ne magabatan al'umma kuma mafi tsarkin cikinsu, rayuka ne wadanda Allah Ya tafiyar da dauda ga barinsu kuma Ya tsarkake su matukar tsarkakewa. Ba a mayar masu da addu'a, ba a kuma karyata wata maganarsu. Daga nan za mu fahimci cewa dukkan abin da ya zo mana daga Ahlulbaiti (a.s) yana gudana ne bisa wannan matsaya (ta tsarki da fifiko) sawa'un wani tunani ne ko shari'a ko ruwaya ko tafsiri ko shiryarwa da fuskantarwa. Domin su ne magaskanta cikin maganarsu da harkar rayuwarsu da kuma tafarkinsu.

Da Ahlulbaiti (a.s) ne Alkur'ani ya kalubalanci abokan gaba Musulunci, ya sanya masu jayayya da su su ne makaryata abubuwan bijirowar tsinuwa da azaba; "…sa'an nan kuma mu sanya la'anar Allah a kan makaryata".

Shakka babu da ba don an lamunce mana tabbatuwa da kuma gaskiya cikin abin da yake fitowa daga gare su ba, da Allah bai ba su wannan daukaka ba kuma da Alkur'ani bai yi furuci da wannan ba.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 next