Ahlul Baiti



3.  Tafsirin Alkur'ani da hankali mai lizimtar Alkur'ani da Sunna.

Haka nan muke samun cewa tafsiri yana da asasai da dokoki, kuma abin da ya tafo na tafsirai wanda za a cewa ra'ayin mutum ya shige shi, ko kuwa an dauki wasu nazarce-nazarcen ilmi wadanda mai tafsirin ya yi zamani da su, ko ra'ayoyin falsafa da ilmin akida, ko abin da aka danganta shi da ruwayoyi raunana ko ma wadanda sanadinsu yashashshe ne, ko kuwa masu karo da ayoyin Alkur'anin da suke a sarari ko kuma sunna tabbatatta, ko kuwa tafsirin da mai tafsirin ya daidaita shi da ra'ayinsa da karkatarsa da kuma sauran irin wadannan, dukkansu ababan yarfarwa ne a tafarkin Ahlulbaiti (a.s) da kuma malamai da masu tafsiri wadanda suka bi shiriyarsu. Sau da yawa kuma ana samun cikin tafsiran musulmi, sunna da shi'a, ra'ayoyi da tafsirai wadanda ba su lizimci wannan hanyar ta Musulunci ba, wadanda kuma ba su bayyana ruhin Alkur'ani.

Don haka, ba wa irin wadannan tafsiran kima ba ya inganta, ba za mu kuma rike su mu yi aiki da su ba, sai dai wanda ya tabbatar wa kansa da ingancinsu.

Mai tafsiri kuwa ko wane ne shi, Alkur'ani hujja ce akansa, ba shi ne hujja a kansa ba. Kuma ba zai zamo hujja kan musulmi ba face da gwargwadon abin da ya dace da katari da abin da ya gano na hakika kawai.

Hakika hani ya zo daga wajen Imamai (a.s.) kan magana ba da wani ilimi ko hujja ba. An ruwaito Imam Bakir (a.s.) yana cewa:

"Abin da kuka san shi to ku fade shi, abin da kuwa ba ku sani ba to ku ce "Allah Shi Ya fi sani". Lalle mutum yana tuzgo aya daga Alkur'ani ya fadi cikin tuzgowar da ya yi, faduwar mai nisan fiye da tsakanin sama da kasa([115])".

Imam Sadik (a.s.) ya ce:

"Ko wane abu ana komar da shi zuwa ga Littafin Allah da Sunna([116])".

Sunnar Annabi (s.a.w.a) A Mazhabar Ahlulbaiti (a.s)

"Allah Ya ni'imta bawan da ya ji maganata sannan ya haddace ta ya kiyaye ta ya kuma bayar da ita (ga wasu) kamar yadda ya ji ta. Sau da yawa ana samun mai daukar ilmi, amma ba malami ba, sannan kuma sau da yawa ana samun mai daukar ilmi ya zuwa wanda ya fi shi sani([117])".

Baicin Littafin Allah, Sunna ita ce mabubbuga ta biyu daga mabubbugan shari'a, wadanda musulmi suke dogara da su wajen fitar da hukumce-hukumce da dokoki da ka'idojin Musulunci. Ita Sunna tana daukar nauyin bayani da faiyacewa da kuma tafsirin Littafin Allah da furuci da abubuwan da ya kunsa da kuma abubuwan da ya tattara na shari'a da tunani da kuma tarbiyya. Shi nassi na Alkur'ani yana dauke da wata wadata da arziki na tunani da shari'a, mai girma kuma dauwamammiya, ita sunna kuwa ta dauki nauyin bayyana wannan arziki da gamar da shi. Lalle hankula ba za su iya riskar Littafin Allah tamkar yadda Sunna take riskar shi tana bayyana shi ba. Manzon Allah (s.a.w.a.) shi aka yi wa zance da wahayi, shi ne kuwa masanin abin da ke cikin Littafin Allah mai girma na daga abin da suka shafi hukumce-hukumce da ababen fahimta daga ciki da kuma manufofin da yake da su.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 next