Ahlul Baiti



Da wannan fantsamar ra'ayoyin siyasa masu sassabawa da fitinu da yake-yake na cikin gida, al'umma ta fuskanci hadari mai munin gaske. Ahlulbaiti (a.s), a matsayinsu na jagororin al'umma, sun kasance mafus-kanta da tushen sakon Musulunci wanda duk wata mishkila ta akida da tunani wacce ta kalubalanci musulmi ana iya warware ta a hannunsu. Domin wannan matsayi nasu na matabbacin tafarkin gaskiya, musulmi suna bin ra'ayinsu da riko da matsayin da suka dauka kan al'amurra. Face wadanda suka damfaru da masu iko, masu kare ayyukansu domin biyan bukatar kansa.

A nan za mu yi dubi cikin tafarkin Ahlulbaiti (a.s) akan abubuwan da suka shafi ayyukan siyasa.

Tafarkin Ahlulbaiti (a.s) Kan Ayyukan Siyasa

Duk wanda ya bibiyo salon siyasar Ahlulbaiti (a.s) da gwagwarmayarsu ta bayyane da ta boye a tsawon karno-ni biyu da rabi zai iya gano cewa aikin da suka yi na siyasa yana bisa ginshikai kamar haka:

(1). Tarbiyyantar da al'umma kan kin zalunci da tabbatar da manufar adalci da bayyana fikirar imamanci da siyasa da fayyace rukunan hukumci da shugabanci cikin addinin Musulunci. Sun yi haka ne domin karfafa fahimtar siyasa ga al'umma da karfafa kulawarta da kiyayyarta ga azzalumai, da farkar da ita daga barci. Wanda ya yi bitar abin da Ahlulbaiti (a.s) suka ruwaito suka watsa daga Manzon Allah (s.a.w.a.) dangane da wannan al'amari, zai gane muhimmancin wannan mataki wajen farfado da ruhin siyasa da kiyayewa ta Musulunci. A nan za mu ambaci wasu daga cikin ruwayoyin da suke magana dangane da shugabanci da kuma nauyin da suka hau kan shugaba musulmi, da kuma kyamar da Musulun-ci yake wa zalunci da kuma kira zuwa ga adalci, don mu fahimci fikira da tunanin Ahlulbaiti (a.s) wajen fada da zalunci da kuma kwadaitar da al'umma zuwa ga canji da kuma motsi na siyasa.

An ruwaito daga Imam Muhammad Bakir (a.s.) cewa wani dattijo daga kabilar Nakh'a ya ce:

"Na ce wa Abu Ja'afar (a.s.) cewa: Ni na kasance gwamna ne tun zamanin Hajjaj har yau din nan, shin za a karbi tuba ta? Sai na yi shiru, sannan na sake maimaita wannan tambayar, sai yace min: "A a; har sai ka mai da wa duk wani mai hakki, hakkinsa([211])".

Abu Hamza al-Thumali ya ruwaito daga Imam Abu Ja'afar al-Bakir (a.s.) cewa:

"Yayin da Aliyu bn Husaini (a.s.) ya zo cikawa sai ya rungume ni ya zuwa kirginsa sannan ya ce: "Ya dana, ina maka wasicci da abin da babana (a.s.) ya mini wasicci yayin da cikawa ta zo masa, kuma da abin da ya ambata cewa babansa ya yi masa wasicci. Ya ce: Ya dana, na hane ka zaluntar wanda ba shi da mai taimako kanka sai Allah([212])".

Imam Sadik (a.s.) ya ce:

"Babu zaluncin da yafi zaluncin da wanda aka zaluntan ba shi da mai taimakonsa a kan shi sai Allah Mai Girma da Daukaka([213])".

Imam Sadik (a.s.) ya ruwaito daga kakansa Manzon Allah (s.a.w.a.) yana cewa:



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 next