Ahlul Baiti



Don aka ne suka yaki bidi'oi da bata, suka yi kira da a lizimci Littafin Allah da Sunna da sanya Littafin Allah ya zama shi ne ma'aunin Sunnar Annabi (s.a.w.a). Sun yi hakan ne domin Littafin Allah abin kiyayewa ne daga karkatarwa da jirkita - Alhamdu lillahi - kiyayye ne kamar yadda Jibrilu (a.s.) ya isar da shi ga Annabi Amintacce Muhammadu (s.a.w.a).

"Lalle Mu muka saukar da Ambato (Alkur'ani) kuma lalle Mu Masu kiyaye shi ne".

Saboda haka, babu hannun jirkitawa ko coge ko wasa da ya taba shi. Domin haka ne ma muke samun Amirul Muminina (a.s) yana cewa:

"Ya ku mutane! Farkon aukuwar fitinu (na daga) son zuciya wadanda ake bi da hukumce-hukumce fararru (wato na bidi'a) wadanda ake sabawa Littafin Allah wajen binsu, mutane suna jibintar wasu mutane wajen bin wadannan hukumce-hukumce. Da dai ita bata tsantsarta take, da ba ta buya ba ga mai hankali, da kuma gaskiya tsantsarta take, da sabani bai samu ba. Amma ana daukar wani abu a nan, a dauki wani a can, sai a cudanya su, sannan su zo tare. A nan ne Shaidan ya rinjaye majibantansa, wadanda kuwa kariya ta gabata gare su daga Allah suka tsira([118])".

Abu Basir, daya daga cikin sahabban Imam Sadik (a.s.) ya ruwaito cewa: "Na ce da Abu Abdullahi (a.s.) cewa: Wadansu abubuwa suna taho mana, mu ba mu san su cikin Littafin Allah ko Sunna ba, to za mu dube su? Sai ya ce: "A'a, amma kai ko ka dace ba za a sakanta maka ba, idan kuwa ka yi kuskure to ka yi wa Allah Mai Girma da Daukaka karya([119])".

Sannan ya ce (a.s.): Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce:

"Dukkan bidi'a bata ce, kuma dukkan bata cikin wuta take".

Abdullah bn Abi Ya'afur ya ce: "Wata rana na tambayi Abu Abdullah (a.s.) game da sassabawar hadisai, wadanda muke amincewa da wadanda ma ba mu amince musu suna ruwaitowa", sai ya ce:

"Idan hadisi ya zo muku kuma kuka sama masa wata shaida daga Littafin Allah ko wata magana ta Manzon Allah (s.a.w.a.), (to ku karba) idan kuwa ba haka ba to wanda ya kawo muku hadisin ya fi cancanta da shi([120])".

An samu daga Ayyub bn Al-Hurr ya ce: "Na ji Abu Abdullah (a.s.) yana cewa:

"Duk wani abu ana iya masa raddi in ban da Littafin Allah da Sunna, to duk hadisin da bai dace da Littafin Allah ba, to kyalkyali ne kawai([121])".



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 next