Ahlul Baiti



Wannan sahabin ya ruwaito cewa: Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce da shi:

"Za ka rayu har ka hadu da wani da nawa daga Husaini, ana ce da shi Muhammadu, yana tsaga ilimi tsagawa. To idan ka hadu da shi ka isar masa da gaisuwa daga gare ni([139])".

Wannan sahabi kuwa ya riski Imam Bakir (a.s.) alhali yana yaro, sannan kuma ya isar da wannan gaisuwa ta Manzon Allah (s.a.w.a.) gare shi.

Lallai a cikin wannan shaida ta annabta da wannan sanarwa, akwai wadatarwa wajen bayyanar da mukamin wannan Imami da dogaro da shi da komawa zuwa gare shi da karbar hukumce-hukumce daga gare shi. Lokacin rayuwarsa, Imam Bakir (a.s.) da dansa Imam Sadik (a.s.) su ne yanki mafi wadata daga dukkan tarihin Musulunci wajen hadisi da ruwaya da kuma sanar da ilmummukan Musulunci.

Hakika malamai da maruwaita da malaman tafsiri da masu neman ilmummukan Musulunci daban-daban a wancan yanki zamanin suna yi wa Imam Bakir kallon kololuwar da tafi kowacce, kuma ilmin da ba wani ilmin da daukakarsa ta kusaci nasa.

Ibn Ahmad al-Hanbali ya siffanta shi da cewa:

"Abu Ja'afar, Muhammadu al-Bakir ya kasance daga malaman Madina kuma ana ce da shi bakir ne domin ya tsaga ilmi wato ya tsaga shi ya sanar da asalinsa ya kuma fadada cikinsa([140])".

Ibn Jawzi ya nakalto daga wani shugaban Tabi'ai, Ada, wata maganar da ya yi kan Imam Muhammad al-Bakir (a.s.) cewa:

"Ban taba ganin malamai suna kaskantar da kai cikin ilminsu kamar yadda na gani a gaban Abu Ja'afar al-Bakir ba([141])".

 



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 next