Ahlul Baiti



Abul Abbas Saffah ya yi kokarin kashe Imam domin saninsa da mukaminsa na jagoranci da goyon bayansa ga bijirewa mahukunta. To amma Allah Ya kare shi daga sharrinsa, duk kuwa da cewa ya taba kiran Imam din daga Madina zuwa garin Hira da ke kasar Iraki, inda ya tsananta masa da kuma sanya shi karkashin 'yan leken asiri.

Yayin da Abu Ja'afar Mansur ya gaji Al-Saffah, shi ma ya ji tsoron matsayin Imam Sadik (a.s.) kamar yadda magabatansa suka ji, sau da yawa ya kan kira Imam (a.s.) daga Madina zuwa Iraki.

Ga yadda yake siffanta karfin Imam a fagen siyasa da tasirinsa kan masu gwagwarmaya, inda ya ke cewa:

"Wannan bakin cikin (yana nufin Imam Sadik) da rike makoshin halifofi, korarsa ba ta halalta, kisan sa ba ya halalta. Ba don mun hadu da shi a bishiya mai kyakkyawan tushe, mai rassan da suka gabata, mai dadadan 'ya'ya, an kuma albarkaci zuriyarta aka tsarkake ta cikin Littattafai ba, da an sanya shi cikin mummunan karshe, saboda labarin da muka samu na tsananin aibantamu da mummunan magana da yake fada game da mu ([244])".

Wannan shi ne matsayin Imam Sadik (a.s.) da aikin da ya yi na bijirewa azzaluman mahukunta, da goyon bayan masu yunkurin kawo gyara.

Daga nan sai zamanin Imam Musa bn Ja'afar Kazim (a.s), dan Imam Sadik (a.s.), a lokacinsa cutar da musulmi da karkata addini da kwadaitar da mutane da dukiya sun tsananta a hannun Abbasiyawa. Don haka ne Imam (a.s.) ya kasance jogora wajen gyaran al'amarin Musulunci.

An sanya Imam (a.s.) karkashin leken asiri a zamanin Mansur wanda shi ya kai matuka wajen zaluntar Alawiyyawa da kwace dukiyoyinsu, da gina turakun gadoji da kadarkai da soraye a kansu da ransu, da azabtar da su cikin kurkuku.

To amma bayan da Muhammad Al-Mahdi ya gaji sarautar Abbasiyyawa sai tsoransa ga Imam Kazim ya yi tsanani, don haka sai ya kirayi Imam (a.s.) daga Madina zuwa Bagadaza domin ya hukunta shi. Al-Mahdi ya sa aka rufe Imam Kazim (a.s.) a kurkuku har zuwa wata rana da halifan ya ga Imam Ali bn Abi Talib (a.s.) a mafarko yana ce da shi:

/h3>

"To, shin, kuna fatan idan kun juya za ku yi barna a cikin kasa, kuma ku yanyanke zumuntarku?" (Surar Muhammadu, 47: 22)

Wannan sai ya tsoratar da Mahdi ya fitar da Imam Kazim (a.s.) daga kurkuku.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 next