Ahlul Baiti



"Idan na dubi Ja'afar bn Muhammad na kan gane cewa shi daga tsatson Annabawa ya fito".

Shahararren malamin tarihin nan Ya'akubi ya siffanta Imam Sadik (a.s.) da cewa:

"Ya kasance mafificin mutane, mafi ilmin addinin Allah. Mazowa ilmi wadanda suka ji daga gare shi sun kasance idan za su ruwaici wani abu daga gare shi su kance; 'Malam ya ba mu labari([145])'.

Wannan dan haske ne kadan daga sanarwar malamai da maruwaita da masu hadisi da kuma shaidarsu mai bayyana matsayin Ahlulbaiti (a.s) da bigirensun nan na ilmi da imani madaukaki.

7- Imam Musa bn Ja'afar al-Kazim (a.s.):

Batun kuma Imam Musa bn Ja'afar (a.s.) kuwa, shi ne dan Imam Ja'afar Sadik (a.s.). Ya sami tarbiyya cikin kulawan babansa wanda daga gare shi ne Imam Musa Kazim ya dibi ilmi da tsantsaini da kyawawan dabi'u. Saboda haka ne ma babansa ya masa shaida da cewa mai girman alkadari da madaukakin matsayi, da kuma cewa dansa Musa shi ne shugaban Ahlulbaiti (a.s), shi ne Imami wanda za a koma gare shi domin karbar ilmomi da masaniya.

Hadisi ya zo daga gare Imam Sadik din yana fadawa wani sahabinsa cewa:

"Lallai wannan da nawa da ka gani, da za ka tambaye shi abin da yake tsakanin bangwayen Littafi guda biyu (Alkur'ani) da ya ba ka amsa da ilmi cikakke([146]).

Malaman Ilmul Rijal da na tarihi sun siffanta shi da cewa shi malami ne mai gaskiya kuma mai ibada ne wanda ya shahara da tsantsaini da takawa da girman al'amari da madaukakin halin kwarai. Za mu ambaci abin da Hafiz al-Razi ya fadi cikin littafinsa na Ilmul Rijal kan irin wannan shaidar, inda yake cewa:

"Musa dan Ja'afar dan Muhammad dan Ali dan Husain dan Ali dan Abu Dalib ya yi ruwaya ne daga babansa, shi kuma dansa Ali bn Musa da dan'uwansa Ali bn Ja'afar sun ruwaito daga gare shi, ya ce; Na ji babana yana fadawa Abdurrahman cewa: An tambayi babana game da shi sai ya ce: Mai gaskiya ne, mai yawan gaskiya, shugaba daga shuwagabannin musulmi([147])".



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 next