Ahlul Baiti



"Digadigan bawa ba za su gushe ba har sai an tambaye shi abubuwa hudu: Kan rayuwarsa, yadda ya karar da ita; da jikinsa, yadda ya tsufar da shi, da dukiyarsa, yadda ya kashe ta da inda ya same ta da kuma soyayyarmu, Ahlulbaiti([85])").

A wata ruwayar kuma, Manzon Allah (s.a.w.a.) yana shiryar da al'ummarsa zuwa ga Ahlulbaitinsa, yana kuma bayyana matsayinsu na ilmi, da kuma fuskantar da al'ummar zuwa gare su yayin da fitinu suka tsananta, ra'ayoyi kuma suka sassaba. Yana gwama su da Littafin Allah, domin su ne malamai masu bayyana abin da Alkur'ani ya kunsa, masana hakikaninsa da abubuwan da ya tattara.

(Dabarani ya fitar da hadisi daga Al-Mudallabi bn Abdullahi bn Handabi daga babansa, ya ce: "Manzon Allah (s.a.w.a.) ya yi mana huduba a Juhfa, ya ce: "Ashe ban fi ku cancanta ba a kan kanku", sai suka ce: "Haka nan ne Ya Manzon Allah". Sai ya ce: "To ni mai tambayar ku ne kan abubuwa biyu: kan Alkur'ani da Ahlulbaitina([86])").


Alkur'ani Mai Girma A Wajen Malaman MazhabarAhlulbaiti (a.s)

"Lalle Mu ne, Muka saukar da Ambato (Alkur'ani), kuma lalle Mu, hakika masu kiyayewa ne gare shi". (Surar Hijr, 15: 9)

Alkur'ani littafin Allah ne da wahayinSa abin saukarwa a kan AnnabinSa mai daraja, Muhammadu dan Abdullahi (s.a.w.a). Littafin da Allah Ya kiyaye shi daga jirkita da gurbata. Wannan wahayin Allah tsarkakakke, wanda hannun mai jirkitawa bai taba shi ba, duk wata barna bata samunsa, ko ta baya ko ta gaba. Shi a yau yana nan kamar yadda ya sauko wa Manzo Amintacce (s.a.w.a), ba tare da wata tawaya ko kari ba. Shi ne mabubbugar shari'a, daga gare shi ake fitar da hukumce-hukumce, shi ne ma'auni sunna, magwajin fahimta da tunani, shi ne mabubbugar wayewar ilmomin Musulunci kana kuma tushen alherin dan'Adam da tsirarsa.

Hakika musulmi sun zazzaga da Alkur'ani tsakanin-su, daga tsara zuwa wata tsarar, suna nakaltar sa da kiyayewa da kula da shi kamar yadda Jibrilu (a.s.) ya saukar da shi ga Manzon Allah (s.a.w.a.). Wannan kuwa shi ne abin da musulmi suka dace a kai, kamar yadda suka hadu a kan karyata ruwayoyi raunana na karya wadanda suka sabawa wannan ijma'i na malamai kan rashin gurbatan Alkur'ani ta kowane bangare.

Babban malamin tafsirin nan wanda ya rubuta shahararren littafin tafsirin nan na Majma'ul Bayan fi Tafsiril Kur'an, Allama Shaikh Abu Ali al-Fadhl bn Hasan Dabrisi([87]) (Allah Ya daukaka mukaminsa), wanda ake daukar tafsirinsa a matsayin mabubbuga kana abin komawa ga malamai da masu tafsiri, ya ce:

"Akwai irin wadannan maganganu (marasa tushe) kan kari ko ragi cikin Alkur'ani, da ba sa ma bukatan magana a kansu. To amma dangane da kari, an hadu kan cewa rashin ingancin hakan, amma batun ragi, wasu jama'a daga cikin abokanmu da wasu mutane daga cikin 'yan Sunna sun ruwaito cewa akwai canji ko tawaya a cikin Alkur'ani. To amma ingantacciyar magana a gurinmu ita ce sabanin hakan (wato babu wata tawaya ko ragi a cikin Alkur'ani), hakan kuwa shi ne abin da Murtadha([88]) (Allah Ya tsarkake ruhinsa) ya bayyana ya kuma yi bayani a kai. A wurare da dama ya ambata cewa ilimin da ake da shi kan ingancin nakalto Alkur'ani kamar ilmin da ake da shi kan garuruwa, manyan abubuwan da suka faru, shahararrun littattafa da rubutattun wakokin larabawa, lallai an sami kula mai tsanani, bukata kuwa ta tabbata kan nakaltar Alkur'ani da kiyaye shi. Bukatar da kular sun kai matsayin da nakalto shahararrun littattafa da wakokin da muka ambata ba su samu ba, domin Alkur'ani mu'ujizar annabta ne, a nan ake daukar ilmomin shari'a da hukumce-hukumcen addini. Malaman Musulunci sun kai matuka wajen kiyaye shi da kare shi har sukan san duk abin da a ka saba cikinsa game da li'irabinsa, kira'arsa, haruffa da kuma ayoyoyinsa, to ya ya zai yiwu a ce an jirkita shi ko kuma an tauye shi duk da wannan kula mai tsanani da kuma tsarewa matsananciya..."

Ya kuma kara da cewa: "Lalle ilmi a kan tafsirin Alkur'ani da sassaninsa da kuma ingancin nakalto shi kamar ilmi ne a kan jumlarsa, kuma hakan yana bisa tafarkin abubuwan da aka sani ne bisa larura cikin littat-tafai wallafaffu, kamar littafin Sibawaihi da Al-Mazanni. Masu kula da wannan sha'ani (nahawu) sun san littattafan nan a fasalce tamkar sanin da suka yi musu a jumlace, ta yadda da wani zai shigar da wani babi na nahawu cikin littafin Sibawaihi, wanda da baya ciki, to da sun gane da kuma fahimtar cewa an sanya shi ne cikin littafin daga baya, ba daga cikin asalin littafin yake ba, haka nan ma yake game da littafin Al-Mazanni. Kuma sananne abu ne cewa kula da nakalin Alkur'ani da tsare shi, yafi gaskata bisa kula da tsare littafin Sibawaihi da kuma Diwanin mawaka".



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 next