Ahlul Baiti



(3). Gwargwarmaya da abin da ya shafi amfani da karfi: Wajibcin umurni da aiki mai kyau da hana mummuna wani ginshiki ne wanda ya tabbatar da gwagwarmaya domin kawar da zalunci, kuma an lizimta da shi ga musulmi.

Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce:

"Shugaban shahidai shi ne Hamza da kuma mutumin da ya mike ya umarci sarki azzalumi (da kyakkyawan aiki) ya hana shi (mummuna) sannan sarki ya kashe shi".

Duk wanda ya bibiyi tsarin rayuwar Ahlulbaiti (a.s) a fagen siyasa da sabawa zaluncin da suka yi, zai ga cewa hanya ce guda wajen sabawa zalunci da kira zuwa ga gyara da gwagwarmaya. Gwagwarmaya ta faro ne a zamanin mulkin Mu'awiyyah dan Abu Sufyan, yayin da ya dora dansa Yazid a kan wuyar al'ummar musulmi duk da cewa bai cancanci shugabanci ba kuma ya rasa dukkan sharuddansa. Wannan ta'asa ta janyo fasadi da kaucewar al'umma, abin da ya sanya Imam Husaini (a.s.) yin shelar jihadi. Imam (a.s.) ya zauna a Makka na tsawon wata hudu bayan barowarsa birnin Madina, daga bisani sai ya fuskanci kasar Iraki. Can a Karbala ne aka yi gumurzu tsakanin rundunar Yazid da jama'ar Imam Husaini (a.s.) 'yan kalilan, a can tsarkakken jini ya zuba, Imam (a.s.) ya yi shahada. Zubar da jinin Imam Husaini (a.s.) tare da Ahlulbaitinsa da kuma mabiyansa ya girgiza al'umma ya tashe ta daga barcin da take ciki. Wannan kuwa shi ne farkon tawaye wa azzaluman mahukunta masu fakewa da Musulunci don cimma burinsu da warware mubaya'ar jabu da shelar kawar da hukumcin bata-gari mai sabawa rukunan Musulunci. Wannan tawaye wa azzalumai shi ya yaye zanin malaman da suke kiran mutane zuwa kaskanci da mika kai bori ya hau, da gurbata ra'ayin ilahirin jama'a da karfafa cewa sai an lizimci mubaya'ar azzalumi an cika masa alkawari komin lalacewarsa. Wadannan muggan malamai dangin Bal'ama dan Ba'ura sun yi kunnen uwar shegu da fadar Manzon Allah (s.a.w.a.) ce wa: "Ba a karbar rantsuwar mai sabo",

Da kuma fadinsa (s.a.w.a) cewa: "Babu biyayya ga halitta cikin sabon Mahalicci".

Suna yin biris da fadin Allah Ta'ala cewa: "Kuma kada ku karkata zuwa ga wadanda suka yi zalunci, sai wuta ta shafe ku". (Surar Hud, 11:113).

Shi Shugaban shahidai, Imam Husaini bn Ali (a.s.) ya kaddamar da gwagwarmayarsa ne a shekara ta sittin da daya bayan hijira, kuma a wannan shekarar ne ya yi shahada a can yankin Karbala na kasar Iraki. Da wannan ne kuma ya rushe dukkan kiraye-kirayen muggan malamai na rauni gaban hukumomin zalunci da yarda da su. Hakika sautin shahada da jini ya rinjayi na kwadayi da kaskanci.

Imam Husaini (a.s.) ya bayyana wa mutane dalilan fitowarsa da tsarin da yake tafe bisansa da cewa:

"Ni ban fito domin girman kai ko alfahari ba, ba kuma domin barna a bayan kasa ko zalunci ba. Abin da kawai ya fito da ni shi ne neman gyara a cikin al'ummar kakana, Manzon Allah (s.a.w.a.). Ina nufin yin umurni da kyakkyawan aiki da hana mummuna, in kuma bi irin rayuwar kakana da babana ([229])".

Sannan ya ayyana wa mutane siffofin shugaba wanda shi ne ja-gora mai jan ragamar musulmi, da wajibcin tsayuwa don gwagwarmayar sauya mai hukumci a yayin da ya karkace ya bar wadannan ginshikin. Ga abin da Imam Husaini (a.s.) ya rubuta wa mutanen Kufa:

"Ina rantsuwa da cewa ba wani ne shugaba ba face mai hukumcin da ya tsayar da adalci, mai riko da addinin gaskiya, mai tsare kansa bisa (umurnin) Zatin Allah ([230])".



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 next