Ahlul Baiti



Bayan tabbatar wannan da soke dukkan raunanan maganganu na barna, za mu gane cewa tafarkin musulun-ci na asali ya nuna wa musulmi da ma'abuta ilmi da sani hanyar fahimtar Alkur'ani da tafsirinsa da mu'amala da nassin Alkur'ani, ya kuma kayyade mana hanyar. Wannan batu na fahimtar Alkur'ani da tafsirinsa da kuma tawilinsa, batu ne mai tushe, wanda kubutar tunani a Musulunce da ingancin akida da shari'a da masaniyar Musulunci duk sun dogara a kansa ne. Domin duk wani karkata ko takaita ko takaitawa wajen fahimtar Alkur'ani da binciken taskar shari'a da akida da fitar da hukumce-hukumcensa da riskar iliminsa da dokokinsa na zamanta-kewar al'umma da na siyasa, tattalin arziki, tarbiyya, zartar da hukumci da dai sauransu, duk suna kai wa ga karkata da rarrabar musulmi, da kuma yin tawaye ga tsarin asalin addinin Musulunci da tsabtarsa.
Wajibi ne a farkon magana kan wannan batu mai tushe da muhimmanci, mu rarrabe tsakanin tafsiri da tawili.

Tafsiri dai a wajen malaman lugga, shi ne: "Gano ma'anar lafazi da kuma fito da ita([107])".

Tawili kuwa shi ne: "Mai da dayan ma'anoni biyu da lafazi ke iya dauka ya zuwa dacewa da zahirin al'amari([108])".

Ahmad Ridha ya ce: "Kalmar tafsiri an dauko ta ne daga kalmar "fassara" wacce aka ciro ta daga "assifru", shi ne kuwa fitarwa da bayyanarwa. Ana cewa "asfaras subhu" wato asubahi ya bayyana, ana kuma cewa "asfaratil mar'atu an wajhiha" wato mace ta fito da fuskarta, an yi amfani da kalmar "asfara" wajen fitowa.

Ko kuma ace kalmar tafsiri an dauko ta ne daga "fasara-yafsiru" kamar "daraba-yadribu" ko "nasara-yansuru" "fasara-yafsiru-fasran. Fasru tana nufin bayyana da fito da rufaffen abu. Mutum ya kan ce "fasartu" ga abu idan ya bayyana shi([109])".

Shaikh Tabrisi (Allah Ya daukaki mukaminsa) ya fadi cikin gabatarwar tafsirinsa mai daraja wato Majma'ul Bayan fi Tafsiril Kur'an cewa:

"Tafsiri shi ne fito da manufar lafazi mai rikitarwa, tawili kuwa shi ne maidowa da dayan ma'anoni biyu da lafazi ke iya dauka, ya zuwa ga dacewa da zahiri. Tafsiri shi ne bayani".

Abul Abbas Mubarrid ya ce: "Tafsiri da tawili da ma'ana duk daya suke. An ce 'fasru' shi ne fitowa da rufaffe, tawili kuwa shi ne karshen abu da makomarsa, da abin da al'amarinsa yake komawa gare shi... ([110])".

Hanyar Da Ake Bi WajenTafsirin Alkur'ani:

Yayin da tafsiri yake bayanin ma'anar kalmomin Alkur'ani da jumlolinsu da kuma fito da ma'anoni a sarari, sannan kuma sashen kalmomin Alkur'ani da jumlolinsa ana iya fassara su da tafsirin zahiri wanda mai yiyuwa ne ya kasance ya yi nisa da manufa ta hakika ga Alkur'ani, shi kuwa tawili shi ne aikin fito da ma'anar da ake nufi, hakan kuwa ta hanyar mayar da ma'anoni da ke ajiye cikin ayar - bayan jujjuya su tsakanin fuskoki biyu ko fiye([111]) - ya zuwa ga makomarsa. Burin da muke so mu cimma a nan shi ne daidaiton tawili da tafsiri a matsayin sakamako. Shi ne kuwa fayyace ma'anonin Alkur'ani da bayanin abin da Allah Madaukakin Sarki Yake nufin bayaninsa ga bayinSa.

Duk wanda ya yi bitar littattafan tafsiri da tafarkin masu tafsiri, zai samu cewa akwai tazara mai fadi da ramuka masu hadari, wadanda sashin masu fassara suka fada, sai suka karkace daga manufar tafsiri domin hanyoyin tafsirin wadanda suka bi da bayanin tawilin da suka yi wa ayoyin Alkur'ani. Wani lokacin a samu sun dogara da raunanan ruwayoyi da aka sossoka, wani loton kuwa a samu sun bi son zuciya sai su tankwarar da Alkur'ani zuwa ra'ayoyin kungiyoyin da suke bi, da kuma son zuciyarsu kebantacciya. Sai ka ga suna kokarin sa ayoyin Alkur'ani su dace da abubuwan da suka auku a tarihi kuma danganta su ga wadansu daidai-kun mutanen da Alkur'anin ba su yake nufi ba. Kai sun ma nemi su sa ayoyin Alkur'ani su dace da girmama ra'ayoyinsu da karkatar su kebantattu.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 next