Ahlul Baiti



Idan mutum ya yi nazarin al'amarin akidar tauhidi da rassanta da matsalolinta bisa tafarkin Ahlulbaiti (a.s) zai riski tsarkaka da zurfin sha'anin tauhidi, kuma zai gane cewa ginshikin akida da duk wata wayewa shi ne kadaita Allah (S.W.T.). Daga nan za a gane cewa akidar tauhidi ta ginu ne bisa tushen; "Tabbatar da cikakken kamala ga Allah (S.W.T.) da tsarkake Shi daga dukkan tawaya da kuma kore duk wani abokin tarayya ko makamanci ko tamka ko kuma kishiya".

Imam Ali (a.s.) ya kafa tushen wannan mahanga ta tauhidi da cewa:

"Tauhidi shi ne kada ka takaita Allah cikin rayawarka takaitacciya, adalci kuwa shi ne kada ka dora wa Allah tuhuma([166])".

A cikin hadisai da muhawarori masu yawa, Imaman Ahlulbaiti (a.s) sun tabbatar da akidar tauhidi tare da raddi kan rudanin da mabarnata da zindikai kamar su Aldaisani da Ibn Abi Al-Awja'a da ibn Almukaffa da mulhidai da 'yan gullatu da 'yan jabru da tafwid da makamantarsu, suka shigar.

A nan za mu kawo wani sashe na wadannan asasai na tauhidi wadanda suke nuna akidar Alkur'ani da kuma ayyana tushen ilmi, tunani na tauhidi, tsabtansa da kuma asalinsa.

Imam Sadik (a.s.) ya ruwaito Amirul Muminina (a.s) yana cewa:

"Ku nemi sanin Allah ta hanyar Allah, Manzon Allah kuma ta hanyar sakon (Musulunci), wadanda aka ba su shugabanci (Ulul Amri) kuwa ta wajen umurninsu da kyakkyawa da haninsu ga mummunan aiki da adalci da kyautatawa([167])".

Alfath bn Yazid ya ruwaito daga Imam Ali bn Musa Ridha (a.s.) cewa:

"Na tambaye shi kan mafi kankantar sanin Allah, sai ya amsa min da cewa:"shi ne yarda da kuma furuci da cewa babu abin bauta koma bayan Allah, babu makamancinSa, babu tamkarSa kuma Shi Dawwamam-me ne ba mai gushewa ba, da kuma cewa babu wani abu tamkarSa([168])".

Nafi'u bn Al-Azrak ya tambayi Imam Abu Ja'afar, Muhammad Bakir (a.s.) cewa:



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 next