Ahlul Baiti



Sai ya ce masa: "Littafin Allah, gefe yana hannun Allah, gefe kuma yana hannunku, to ku yi riko da shi, ba za ku bata ba, ba za ku canjba ba, da kuma iyalina, mutanen gidana. Hakika Mai Tausayawa, Masani, Ya sanar da ni cewa su biyun ba za su rabu da juna ba har sai sun iske ni a bakin tafki. Na roka musu wannan wajen Ubagijina, saboda haka kada ku gabace su sai ku halaka, kada ku takaita (ga barinsu), sai ku halaka, kada ku sanar da su domin sun fi ku sani([38]).

Sannan sai ya ce: "ashe ba ni ne nafi cancanta ga kowane mumini a kan kansa ba"?

Sai suka ce: "Haka ne, Ya Manzon Allah([39])".

Daga nan sai ya kama hannun Aliyu bn Abi Talib (a.s.) ya daga sama har mutane suka ga farin hammatarsa([40]), ya ce:

Ya ku mutane! Allah Shi ne Majibincina, ni kuma ni ne majibincinku([41]). To duk wanda na ke majibincinsa, wannan Aliyun majibincinsa ne. Ya Allah! Ka jibinci wanda ya jibince shi, Ka yi gaba da wanda ya yi gaba da shi([42]), Ka taimaki wanda ya taimake shi, Ka wulakanta wanda ya wulakanta shi([43]), Ka so mai son sa, Ka ki wanda ya ki shi([44])".

Sannan sai ya ce: "Ya Allah Ka shaida([45])".

Ba su (Manzon Allah da Aliyu) rabu ba har sai da Allah Ya saukar da wannan aya:

 (اليَومَأَكْمَلْتُ لَكُمْ دِينَكُم وأَتْمَمْتُ عَلَيْكُم نِعْمَتي وَرَضِيتُ لَكُمُ الإسْلاَمَ دِينًا )

"A yau Na kammala muku addininku, kuma na cika muku ni'imaTa a kanku, kuma Na yarda da Musulunci ya zama addini a gare ku". (Surar Ma'ida, 5:3)

Sai Manzon Allah (s.a.w.a.) ya ce:



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 next