Ahlul Baiti



Yayin da kuma aka tambaye shi kan ganin Allah (S.W.T.) sai ya tsarkake Allah ga barin ganuwa. Ga tambayar:

"Ya Amirul Muminina! Shin ka ga Ubangijinka lokacin da kake bauta masa? Sai ya ce: "Kaitonka! Bana bautar Ubangijin da ban ganshi ba", sai ya ce masa to yaya ka gan shi?, sai Imam (a.s.) ya amsa masa da cewa: "Tir da kai, idanu ba sa riskar Allah da gani irin na ido, sai dai zukata sun gan Shi da matabbatan imani([175])".

Muhammad bn Hakim ya ce: "Abul Hasan Musa bn Ja'afar (a.s.) ya yi rubutu ya aike wa babana cewa: "Allah (S.W.T.) Ya daukaka, girmanSa ya buwaya ga barin riskar ainihin siffarsa. Ku siffanta Shi da abin da Ya siffanta kanSa da shi, ku kuma kame ga barin koma-ba-yanSa([176])".

Al-Mufaddal ya ce: 'Na tambayi Abul Hasan wani abu kan sifa, sai ya ce: "Kada ku ketare abin da ya ke cikin Alkur'ani([177])".

Abdur Rahman bn Atik Alkasir ya ce: 'Na rubuta tambaya zuwa Abu Abdullah al-Sadik (a.s.) ta hannun Abdul Malik bn A'yun cewa:

"Wasu mutane a Iraki suna siffanta Allah da wani yanayi da kuma kama, to idan ka yarda, Allah Ya sanya ni fansarka, ina so ka rubuto min da bayani kan ingantac-cen matsayi kan tauhidi. Sai ya rubuto mini da cewa: "Ka yi tambaya - Allah Ya jikanka - kan tauhidi da kuma abin da wadannan mutane suke fadi. Daukaka ta tabbata ga Allah Wanda babu wani abu tamkarSa, Shi ne Mai ji, Mai gani. Allah Ya daukaka ga barin siffantawar masu siffantawa, wadanda suke kamata Allah da halittarSa, masu kage wa Allah. To ka sani -Allah Ya rahamshe ka- cewa ingantacce tafarki wajen tauhidi shi ne abin da Alkur'ani ya saukar da shi na siffofin Allah Mai Girma da Daukaka. To ka kore ga barin Allah (S.W.T.) dukkan korewa da kamantawa, domin babu korewa ba kuma kamantawa. Shi ne Allah Tabbatacce Ya daukaka ga barin siffantarwar masu siffantawa. Kada ku ketare Alkur'ani ku bata bayan (cikakken) bayani([178])".

Batun dayantuwar zatin da tsarkake shi ga barin kama da halitta kuwa, Hamza bn Muhammad ya ce: 'Na rubuta tambaya ga Abul Hasan Al-Kazim (a.s.) kan jiki da kama (da ake danganawa ga Allah), sai ya rubuto min cewa:

"Tsarki ya tabbata ga Wanda babu wani abu tamkarSa, ba jiki babu kama([179])".

Haka nan muke karanta tauhidi tsarkakakke, kubutacce na Allah (S.W.T.) a mazhabar Ahlulbaiti (a.s) da karantarwarsu da ke nuna ainihin ruhin Alkur'ani da abubuwan da yake tattare da su, da abin da ayoyinsa suka kunsa. Da wannan ne suka tabbatar da akidar tauhidi, suka kore barnace-barnace da shubuhohi da bata wadanda aka jarrabi tunanin Musulunci a wancan lokacin. Haka kuma wannan bayani yake raddi kan batattu da karkatattun 'yan gulatu(*) (masu wuce gona da iri wajen soyayya), 'yan Mufawwida (masu cewa an bar dan'Adam haka kawai a sake komai yayi daga gare shi ne), 'yan Mujassima (masu siffanta Allah da jiki), 'yan Hululi (masu akidar cewa Allah Yana shiga wasu halittu) da kuma masu akidar haduwa, wato Allah Ya hadu da halittanSa suka zama abu guda.

Haka kuma bayanan Ahlulbaiti (a.s) sun fayyace al'amurra wa wadanda suka shiga rudani suka cudanya tafarkin Ahlulbaiti (a.s), tsarkakakke na gaskiya, wanda bai yarda da karairakin 'yan gulatu da 'yan mufawwida da 'yan hululi ba wadanda suka yi da'awar suna bin Ahlulbaiti (a.s), da wadancan kungiyoyi na bata.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 next