Ahlul Baiti



"Idan ranar alkiyama ta zo mai kira zai yi kira: Ina azzalumai da mataimakansu; wanda ya shirya masu kurtun tawada ko ya daure musu wata jaka ko ya fere musu kan alkalami, ku tara su tare da azzalumai ([224])".

Kyakkyawan misalin yankewa azzalumai shi ne abin da A'imma (a.s.) suka yi da matakan da suka dauka dangane da zalunci da azzaluman mahukuntan Umayyawa da Abbasiyawa a zamanin Imam Sajad, Imam Bakir, Imam Sadik, Imam Kazim, Imam Ridha ([225])(*), Imam Jawad ([226])(**), Imam Hadi da kuma Imam Hasan Askari (a.s.).

A wannan lokacin A'imma (a.s.) sun gamu da wahalhalu daban-daban daga mahukunta, kamar cutarwa da kora da sa ido da shiga kurkuku da matsi da tsoratarwa, za mu kawo kadan daga cikin irin wadannan abubuwa a cikin wannan littafi.

A matsayin misali na irin wannan yankewa, shi ne matsayin da Imam Sadik (a.s.) ya dauka dangane da halifan Abbasiyawa Abu Ja'afar Mansur wanda ya shahara da mugun hali da zubar da jini da zalunci ga zuriyar Imam Ali (a.s.). Malaman tarihi sun rubuta cewa, wata rana Mansur ya rubuta wasika zuwa ga Imam Sadik (a.s.) yana neman zama da shi don kokarin sanya shi cikin malaman hukuma. Sai Imam yaki duk kuwa da halin tsoratarwa da kaushin halin da mahukuntan suke nunawa.

Ga abin da Mansur ya rubuta:

"Me zai hana ka ziyarce mu kamar yadda mutane suke ziyartarmu"?, sai Imam (a.s.) ya rubuta masa cewa:

"Babu abin da muke tsoronka dominsa, babu wani abu daga sha'anin lahira a gare ka wanda zai sa mu kaunaci (saduwa da) kai dominsa. Ba ka kuma cikin wata ni'ima ballantana mu yi maka murna, ba ma kuma ganinsa a matsayin azaba ballantana mu yi maka jaje". Sai Mansur ya rubuto amsa ya ce: "Ka zauna da mu saboda ka yi mana nasiha". Sai Imam (a.s.) ya amsa masa da cewa:"Mai nufin samun duniya ba ya maka nasiha, wanda kuwa yake nufin lahira ba ya zama da kai ([227])".

Haka nan dai matsayar A'imma (a.s.) da raddinsu ya kasance ga mahukuntan da ba sa tsai da shari'a, ba su lizimtar ginshikanta.

To haka nan ma malaman fikihun mazhabar Ahlulbaiti (a.s) suka bi tafarkin Imamansu wajen yanke hulda da azzaluman mahukunta ta hanyar fatawoyinsu masu haramta taimakawa azzalumai ko karbar aikin hukumominsu. Suna kawo wannan ne galibi a babin makasib wato hanyoyin neman abin masarufi. Bari mu kawo maganar Shahid Muhammad bn Jamal(*) Makki al-Amuli wanda aka fi sani da Shahidul Awwal (Allah Ya rahamshe shi) yayin da yake kawo sana'oi haramtattu cewa: "Da taimakon azzalumai cikin zalunci" (yana daga cikin haramtattun sana'oi), shi kuma mai sharhin littafin ya ce: "Kamar yi musu rubutu da kawo musu wanda suke zaluntarsa da dai makamantansu ([228])".

Malaman sun hana karbar duk wani aiki a hukumar azzalumai sai dai da nufin yi wa Musulunci hidima da tunkude zalunci ga barin bayin Allah, ta yadda dai za a samu wani gyara ko wani amfani ga al'umma.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 next